A ranar Talatar da ta gabata ce ma’aikatan Kamfanin Media Trust Ltd, mai buga jaridun Daily Trust da Aminiya suka karrama tsohon Editan Daily Trust, kuma tsohon Manajan Editan Kamfanin, Malam Nasiru Lawal Abubakar da Editan Kula da Shafuka, Mista Niiyi A. Bulley wadanda suka bar kamfanin bayan shafe shekaru suna aiki.
Malam Nasiru Lawal Abubakar ya kwashe shekara 20 yana aiki da kamfnin, inda ya kai mukamin Manajan Editan kamfanin da ke kula da editoci da bangaren labarai na kamfanin.
- Kamfanin Media Trust ya samu lambar yabo daga Hukumar NACA
- Kamfanin Media Trust ya karrama ma’aikatansa 41
- Gwamna Buni ya jinjina wa Kamfanin Media Trust
Hakazalika shi ma Mista Niiyi ya dade yana jagorantar tsara shafuka.
Da yake jawabi a wajen takaitaccen bikin karramawar, Editan Daily Trust, Malam Hamza Idris ya bayyana tsofaffin ma’aikatan a matsayin jajirtattun ma’aikata, inda ya ce za a yi rashin sadaukar da kai da hakuri da iya zama da jama’a da suke da su.
Ya shawarci ma’aikatan kamfanin su ci gaba da aiki tukuru domin ciyar da kamfanin gaba, kamar yadda tsofaffin ma’aikatan biyu suka yi.
A jawabansu, Malam Nasiru da Mista Niiyi sun nuna godiyarsu ga ma’aikatan kamfanin bisa karramawar da suka yi musu.