Kungiyar Ma’aikatan Wutar Lantarki ta Najeriya za ta ce tsunduma yajin aiki sakamakon cire tallafin man fetur da gwamnatin kasar ta yi.
Ƙungiyar ta ce ta dauki matakin ne bayan da Kungiyar Kwadago ta Kasar NLC ta sanar da matakin tsunduma yajin aiki sakamon cire tallafin man fetur da gwamnatin kasar ta yi, lamarin da ta ce ya haifar da karuwar hauhawar farashin kayyaki a kasar.
- Camfe-camfe 50 da Hausawa suka yi amanna da su
- Benzema ya bar Real Madrid bayan shekara 14 a kungiyar
Shugaban kungiyar mai lura da shiyyar birnin tarayya Abuja da Kogi, Godfrey Aba ya tabbatarwa da cewa kungiyar za ta shiga yajin aikin daga ranar Laraba 7 ga watan Yuni, matukar gwamnatin kasar ba ta janye matakin cire tallafin man ba.
Ya kara da cewa “kungiyar za ta shiga yajin aikin ne har sai gwamnati ta janye matakin da ta dauka.”
A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar mai dauke da sannun mukaddashin sakataren kungiyar na kasa, Dominic Igwebike, ta yi kira ga mambobinta da su yi biyayya ga matakinta na tsunduma yajin aiki a tsakiyar makon da ke tafe.
Ƙungiyar Kwadago ta Kasar, NLC dai ta ce za ta fara yajin aiki tare da zanga-zanga daga ranar Laraba mai zuwa a wani mataki na nuna rashin amincewarta kan cire tallafin man fetur da gwamnatin kasar ta yi.
Sabon Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ne ya sanar da matakin cire tallafin man fetur din a cikin jawabin da ya gabatar cikin makon jiya a lokacin bikin rantar da shi.
Ita ma dai Kungiyar ’Yan Jarida ta kasar, NUJ ta sanar da daukar makamancin wannan mataki a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar.