Gamayyar kungiyoyin lafiya da a takaice ake kira JOSHESU sun bukaci membobinsu da ke aiki a asibitocin gwamnatin tarayya su fara yajin aikin sai-baba- ta- gani daga ranar tsakar daren ranar Talata, 17 ga watan Afrilun shekarar 2018.
Hakan ya biyo bayan gazawar da gwamnatin tarayya ta yi na aiwatar da yarjejeniyar da ta yi da gamayyar kungiyoyin.
Gamayyar kungiyoyin ma’aikatan lafiyar sun hada da kungiyar likitoci da ma’aikatan jinya ta MHWUN da kungiyar nas-nas da ungozoma da manyan ma’aikatan asibitin kwararru na jami’o’i da kungiyar hadakar kwararrun aikin lafiya da kuma kungiyar ma’aikatan da ba na bangaren koyarwa ba na makarantun aikin lafiya ta NASU.
Gamayyara kungiyoyin sun sanya membobinsu cikin ko-ta-kwana don fadakar da membobinsu yiwuwar shiga yajin aiki idan gwamnati ba ta cika alkawarin da ta yi musu ba.