Gwamnatin Kaduna ta umarci ma’aikatanta da su koma bakin aiki daga ranar Litinin, wata uku bayan dokar kullenta na hana yaduwar cutar coronavirus a jihar.
Yayin sassauta dokar a ranar 9 ga watan Yuni, Gwamna Nasir El-Rufai ya ce daga baya za a sanar da tsarin komawar ma’aikatan gwamnatin jihar aiki.
Sanarar da Ofishin Shugaban Ma’aikatan Jihar ta fitar ta ce daga Litinin 20 ga watan Yuli, “Shugabannin hukumomi da Manyan Sakatarori da Manayan Darektoci da Darektoci za su rika aiki daga ranakun Litinin zuwa Juma’a.
“Ma’aikata daga mataki na 14 zuwa sama za su yi aiki a ranakun Litinin da Laraba da Juma’a; yayin da ’yan mataki na bakwai zuwa 13 za su yi nasu a ranakun Talata da Alhamis, duk daga 9.00 na safe zuwa 3.00 na rana”, inji sanarwar.
Sanarwar da Babban Sakataren Ofishin Ibrahim Jere ya fitar ta ce za a rika gudanar da ayyukan ne cikin kiyaye dokokin kariya na cutar coronavirus, sannan ta haramta kai wa ma’aikata ziyara a wuraren aiki.