Ma’aikatan sufurin jiragen kasa sun kudiri aniyar shiga yajin aikin gargadi na kwanaki 3 daga ranar Alhamis 18 ga watan Nuwamba zuwa 20 ga Nuwamba.
Babban sakataren Kungiyar Ma’aikatan Layin Dogo a Najeriya (NUR), Kwamared Segun Esan, ya tabbatar da haka, kuma rahotanni na cewa tuni kungiyar ta sanar da mahukunta shirin shiga yajin aikin.
A baya dai kungiyar masu aikin jiragen kasa ta Najeriya NUR da yar uwarta, ta manyan ma’aikatan hukumar da kuma kamfanin na gwamnati, sun bai wa Gwamnatin Tarayya da Hukumar Kula da Jiragen Kasa ta kasa wa’adin makonni uku don biyan wasu bukatunsu da suka hada da karin albashi da alawus-alawus daga ranar 14 ga watan Nuwamba.
Sauran bukatun sun hada da inshorar lafiya da biyan alawus-alawus na ma’aikatan da suka samu karin girma tun daga 2018 zuwa yanzu.
Kungiyoyin sun ce za su ci gaba da fafutukar ganin cewa an inganta musu albashi saboda a bayyane take cewa tsarin albashin ma’aikatan jirgin kasa shi ne mafi karanci a kasar.