✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’aikatan  jami’o’in Najeriya za su shiga yajin aikin sai Baba ta gani

Muna fatan gwamnatin za ta yi abin da ya kamata kafin karshen wannan zanga-zangar ta kwana uku.

Ma’aikatan Jamai’o’in Najeriya sun daura damarar shiga yajin aikin sai Baba ta gani bayan kammala zanga-zangar lumana ta kwanaki uku da suka fara a fadin kasar.

Shugaban Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’a (SSANU), Muhammadu Ibrahim, ya ce sun yanke shawarar za su shiga yajin aikin ne a ranar  Alhamis sakamakon watsi da bukatansu da Gwamnatin Tarayya ta yi.

A ranar Talata ne ma’aikatan jami’o’in Najeriya suka fara zangar-zangar ta lumana domin yi wa Gwamnatin Tarayya matsin lambar ganin ta waiwayi bukatunsa da suka hadar da shawo kan takaddamar da ta dabaibaye sabon Tsarin Biyan Albashi na bai daya (IPPIS).

Sauran bukatun da kungiyar ma’aikatan ke bukatar gwamnati ta warware sun hada tsarin raba Naira biliyan 40 na alawus-alwawus a tsakanin ’ya’yanta da na kungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU.

Kungiyar ma’aikatan Jami’o’in tare da hadin gwiwar kungiyoyin manyan ma’aikatan jami’o’i SSANU sun fara gudanar da zangar-zangar ta lumana a jami’ar Abuja dauke da alluna masu alamun rashin gamsuwa da matakin gwamnatin tarayya.

Shugaban SSANU ya ce za su dauki mataki na gaba a ranar Alhamis muddin gwamnatin ta yi biris da bukatunsu, inda ya ce wannan zanga-zangar somin tabi ce.

“Idan har gwamnati ta yi watsi ba tare da waiwayi bukatunmu ba, za mu dauki mataki a ranar Alhamis.”

“Don haka muna fatan gwamnatin za ta yi abin da ya kamata kafin karshen wannan zanga-zangar ta kwana uku.”

A nata bangaren, ma’ajin kungiyar ma’aikatan jami’a da basa koyarwa, Sadiya Hassan, ta jaddada cewa kungiyarsu ba ta za ta yi jinkirin gurgunta ayyukan ilimi a fadin jami’o’in kasar ba  idan har gwamnati ta ki jin kira game da bukatun da suka gabatar mata.

A cewarta, “Muna zanga-zanga ne a kan rashin daidaiton da ya dabaibaye tsarin biyan albashi na bai daya da kuma yarjejeniyar da muka kulla da gwamnatin tun a shekarar 2009 wacce har yanzu ba a cika ta ba.”

“Muna kuma gudanar da zanga-zangar ne don nuna rashin amincewa da kin biyan mu alawus dinmu da kuma rashin adalcin da Gwamnatin Tarayya ta yi wajen rabon kudaden alawus wanda ta ce kungiyar ASUU za ta dauki kashi 75 sannan sauran kungiyoyin su dauki kashi 25.

“Hakan ya saba wa yarjejeniyar da muka kulla da gwamnatin a watan Oktoba na cewa kudin na dukkan kungiyoyin ne don haka muke sa ran a yi adalci wajen rabawa.”