Gwamnatin Jihar Gombe ta sanar da cewa za ta soma biyan sabon albashi mafi ƙanƙanta na Naira 70,000 daga ƙarshe wannan wata na Oktoba.
Mataimakin Gwamna kuma Shugaban Kwamitin Tuntuba kan sabon albashi mafi ƙanƙanta, Dokta Manasseh Daniel Jatau ne ya bayyana hakan yayin zantawarsa da manema labarai a ranar Alhamis.
Da yake jawabi bayan ganawa da wakilan ƙungiyar kwadago na jihar, Dokta Jatau ya ce gwamnatinsu ta shirya soma biyan sabon albashi mafi ƙanƙanta daga watan Oktoba wanda tuni ta kafa kwamitin da zai tabbatar an aiwatar da hakan nan da sa’o’i 72.
Mataimakin Gwamnan ya kuma buƙaci ma’aikata da kada su yi jinkiri wajen miƙa masa rahoto kai tsaye muddin ba su ga wani ƙari daidai da sabon tsarin a albashinsu na watan Oktoba ba.
A yayin da yake yaba wa Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya, Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago na jihar, Kwamared Yusuf Aish Bello, ya ce za su yi aiki kafada da kafada da kwamitin da aka kafa domin aiwatar da sabon albashin mafi ƙaranci cikin ƙanƙanin lokaci.