Kimanin ma’aikata 150,000 da ke kwadago a gonakin shayi sama da 200 a Bangladesh sun shiga yajin aikin a ranar Asabar, a cewar Sitaram Bin, wani mamba a kungiyar ma’aikatan ganyen shayi na kasar.
Ma’aikatan ganyen shayi sun bukaci kari da kashi 150 bisa 100 na albashin dala daya da suke karba duk rana, wanda shi ne albashi mafi karanci a duk fadin duniya a cewar masu bincike.
- Babu Messi a jerin ’yan wasa 30 masu takarar lashe kyautar Balon d’Or ta bana
- Mika wuyan ’yan Boko Haram 14,609 ya bar baya da kura
Galibin ma’aikatan ganyen shayin a kasar mai rinjayen musulmi mabiya addinin Hindu ne masu karamin karfi, wanda zuriyar ma’aikata ne da suka shiga aikatau a gonakin ganyen shayi da Turawan Ingila na zamanin mulkin mallaka suka kawo.
Wata ma’aikaciya ta bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa, da kyar albashin ke isarsu siyan abinci, balle sauran kayan masarufi.
A cewar Anjana Bhuyian mai shekaru 50, “A yau, ba za mu iya siya wa iyalanmu ko da shinkafa ba da wannan albashi.
“Ladan da muke samu na aikin kowane wuni ba zai iya sayen litar man girki ba, ballanatana a fara batun siyan magani ko ilimin yara ba.”
Masu bincike sun ce ma’aikatan ganyen shayi – wadanda ke zaune a wasu yankuna masu nisa a kasar – masu gonakin na cin moriyarsu matuka tsawon shekaru da dama.
“An mayar da ma’aikatan ganyen shayi kamar bayi,” in ji Philip Gain, wani darekta a Cibiyar da ke Bincike kan Bunkasa Al’umma da Muhalli da ta rubuta littattafai kan masu aikin ganyen shayi.
“Masu gonakin sun mamaye hukumomin da ke da alhaki kan mafi karancin albashi a kasar, wanda kuma bincikenmu ya nuna ma’aikatan ganyen shayi su ne masu daukan mafi karancin albashi a duniya.”
Ya zuwa yanzu dai kungiyoyin ma’aikatan sun ce suna son a yi karin kashi biyu da rabi na albashin, amma masu gonakin da suke yi wa aiki sun ki amincewa da hakan, suna cewa za su kara dai abin da ya samu.
Kafofin yada labaran kasar sun ambato cewa ma’aikatan sun samar da kilo miliyan 96 na ganyen shayi a bara.
Bangladesh dai tana cikin kasashe mafi talauci a duniya wadda aka dade ana kallonta a matsayin kasar da sai dai kowa ta sa fisshesa, inda shugabanni da masu hannu da shuni ba su damu da rayuwar talakawa ba.
A bana ce Jaridar Dhaka Tribute ta ruwaito, akalla ma’aikata 2,000 ne suka mutu a gobara 26 a cikin shekaru 20 da suka gabata.
Ko a shekarar da ta gabata, sai da wasu yara leburori suka kone da ransu a wata gobara da ta tashi a wata masana’anta.
Fiye da ma’aikatan tufafi 1,100 ne suka mutu a rugujewar ginin Rana Plaza a shekarar 2013 – hatsarin masana’antu mafi muni a tarihin Bangladesh – kuma har yanzu ba a bi musu hakki ba.