Ma’aikatan sufurin jiragen sama a filin jirgi na Malam Aminu Kano sun yi zanga-zangar lumana kan zargin Gwamnatin Tarayya na kokarin cefanar da manyan filayen jirgi na kasar guda hudu da kuma kokarin mayar da su cikin tsarin fansho na kudaden hadaka.
Filayen da batun ya shafa sun hada da na Murtala Muhammad da ke Legas da na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, na Malam Aminu Kano da ke Kano da kuma filin jirgin sama na Fatakawal.
Masu zanga-zangar ta ranar Litinin karkashin gamayyar kungiyoyi hudu da ke cikin Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Najeriya (FAAN), sun bayyana shirin cefanar da filayen a matsayin yunkurin kai su kushewa da ransu, kasancewar ba a yi wa makomarsu tanadi ba a cikin shirin.
“Nan take muna Allah-wadai da yunkurin cefanar da filayen, kada a yaudare ku, Gwamnati so take ta sayar da filayen ga ’yan kasuwa. Wadannan filayen guda hudu na Kano, Legas, Fatakwal da Abuja su ne ginshikan ragowar filaye 18 na Najeriya”, inji Sama’ila Muhammad Alkali, shugaban Kungiyar Manyan Ma’aikatan Sufurin Jiragen Sama ta Kasa (ATSSSAN).
Sama’ila, wanda kuma shi ne Jami’in Hulda da Jama’a na Kungiyar Kwadago ta TUC reshen Jihar Kano ya ce shirin ya kunshi sayar da tashoshi, wuraren ajiye motoci da kuma wuraren karbar kudade na filayen jirgin saman.
A cewarsa wadannan wuraren ne ke samar da kaso 65 cikin 100 na kudin shigar filayen jirgin saman da abun zai shafa.
“A cikin yarjejeniyar, wadanda za su sayi filayen na da damar korar duk ma’aikacin da ba su gamsu da aikinsa ba cikin shekaru biyu. Saboda haka ko da mutum ya shafe shekaru 20 ko 30 yana aiki a wajen, in aka kore shi ya tashi a tutar babu ke nan”, inji shi.
Ma’aikatan sun kuma koka kan cewa sayar da filayen zai kawo kalubale ga harkar tsaro, musamman a daidai lokacin da kasar ke fama da ita.
“Ba ma wanda ya san wa za a sayar wa. Su fa filayen nan suna daya daga cikin iyakokin kasa. Idan ka sayar wa mutane masu zaman kansu, su kawai abin da za su fi mayar da hankali shi ne yadda za su samu riba, ba ruwansu da tsaron kasa. Za ma su iya bari a shigo da makamai matukar za su samu riba”, inji jami’in.
– Tsarin fasho na hadaka
A kan yinkurin shigar da su cikin tsarin asusun fansho na hadaka kuwa, kungiyoyin sun ce gwamnati na shirin yin haka ne ba tare da ta tuntubi dukkannin masu ruwa da tsaki ba.
Ya ce, “Kafin ka mayar da ma’aikaci cikin tsarin, ya kamata ka san asalin abin da yake cikin asusun ajiyarsa. Dole sai ma’aikaci ya adana wani abu a asusun kafin ya koma. Amma idan ka mayar da mu ba tare da sanin makomarmu ba tamkar yinkurin binne mu ne da ranmu.
“Yanzu haka ma’aikatan hukumar mun haura 8,000 kuma har yanzu ministan yana kara dibar sabbabbi. Saboda haka muna kiran ministan da ya yi wa Allah ya kyale mu mu ci gaba da tsohon tsarin da muke ciki,” inji Sam’ila.
Shima da yake jawabi, wani jagoran masu zanga-zangar, Kwamaret Hassan Aliyu ya ce suna kin shirin ne saboda sun ga abin da ya faru da ma’aikatan NEP, NITEL da kamfanin sufurin jiragen Nigerian Airways.
Ya ce kamata ya yi gwamnati ta fitar da kudade domin cike basukan da ake bin su kafin ta tura su cikin tsarin.