Ma’aikatan Ofishin Samar sa Fasfo na kasar Ingila sun tsunduma yajin aikin mako biyar saboda fama da matsalar karancin albashi da kudaden fansho.
Sama da ma’aikata 1,000 na kungiyoyin kwadagon kasar (PCS) a wurare takwas ne suka kulle ofisoshinsu don nuna rashin jin dadinsu da yanayin da suka shiga ciki.
- NAJERIYA A YAU: Gayyatar ’yan IPOB Legas tamkar gayyatar ’yan Boko Haram ne – Lauya
- Dan sanda ya mutu yana kokarin raba fada a Neja
Sakataren kungiyar ta PCS, Mark Serwotka ne ya bayyana haka ranar Litinin.
A cewarsa, za su karkafa shingaye a kofofin shiga ofisoshin a biranen Glasgow da Durham da Liverpool da Southport da Peterborough da Landan da Belfast and Newport a yankin Wales.
Kungiyar ta kuma ce za ta yi amfani da kudaden da ke cikin lalitarta wajen aiwatar da yajin aiki, kuma sun rubuta wa gwamnati wasiku suna bukatar ta dauki mataki a kan lokaci.
Mark ya kuma zargi Ministocin kasar da nuna fifiko ga wasu ma’aikatan gwamnati, musamman na lafiya da malaman makaranta.
Ofishin na fasfo dai ya ce ya zuwa yanzu, dai sun yi aikin Fafo sama da miliyan 2.7 daga farkon wannan shekarar. (dpa/NAN)