✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ma’aikata sun yi barazanar rufe ilahirin makabartun Abuja

Suna yajin aikin ne bayan saboda karin albashi

Ma’aikatan muhalli da ke Babban Birnin Tarayya Abuja sun yi barazanar rufe ilahirin makabartun birnin.

Da farko dai ma’aikatan sun rufe makabartar Gudu da ke Abuja, kafin daga bisani su sake budeta da safiyar Alhamis bayan Fadar Shugaban Kasa ta sa baki.

Fusatattun ma’aikatan dai sun alakanta daukar matakin nasu da kin yi musu karin albashin da hukumar birnin ta yi musu alkawari.

A cewar shugaban Gamayyar Kungiyoyin Muhalli na Abuja (AUPCTRE), Kwamared Muktar Bala, duk da yake kungiyar ta amince ta bude wasu makabartun, amma za ta rufe dukkan ragowar muddin aka gaza cika mata alkawuranta.

Shugaban, wanda ya bayyana damuwa kan yadda hukumar ba ta kula da walwalarsu, ya kuma ce suna jefa rayukansu cikin munanan hadurra a yayin adana gawarwakin da aka tsinta.

“A matsayina na shugaban kungiyoyin, ina tabbatar muku da cewa wannan shi ne matakin da muka dauka, bisa sahalewar uwar kungiyarmu ta kasa.

“Mutane na tunanin kwashe shara ne kawai aikinmu, ba su san cewa hatta gawarwakin da ba a san ’yan uwansu ba mune ke da alhakin kula da su.

“Gawarwakin da suka dade a asibitoci suka kai kamar shekara uku zuwa hudu, mu muke kula da su, duk da ba mu san mene ne asalin abin da ya kashe su ba. Muna shiga hadura masu yawa,” inji Kwamared Muktar Bala.