✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’aikata sun fara yajin aiki kan sabon albashi a Kaduna

Gwamnatin da shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago ba su cimma matsaya kan lamarin ba.

Ma’aikata a Jihar Kaduna, sun fara yajin aiki na mako guda saboda rashin aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi a jihar.

Ƙungiyoyin Ƙwadago na NLC da TUC ne suka bayar da umarnin fara yajin aiki a ranar Litinin.

Shugaban NLC na jihar, Ayuba Suleiman, ya shaida cewar, gwamnatin jihar ta aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashin, amma ta kasa daidaita albashin sauran ma’aikatan jihar.

Sai dai gwamnatin jihar ta musanta hakan, inda ta bayyana cewa ta fara biyan ma’aikatan jihar Naira 72,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi a watan Nuwamba.

Mai Magana da Yawun Gwamnan jihar, Malam Ibraheem Musa, ya ce ƙarin albashi ba zai yiwu ba saboda ƙaracin kuɗaɗen shiga da jihar ke fama da shu.

Ya ce mafi yawan kuɗin da jihar ke kashewa na tafiya ne wajen biyan albashi da kuma biyan bashi.

Musa, ya bayyana cewa kashe ƙarin kuɗaɗe a kan albashi ba zai bar gwamnatin ta yi wa al’umma aiki ba.

Ya roƙi ma’aikatan jihar da su jira zuwa lokacin da abubuwa za su daidaita kafin yi musu sabon ƙari a albashinsu.

Har ila yau, ya ce gwamnatin ta bayar da motoci kyauta ga ma’aikata don sauƙaƙa musu zuwa wajen aiki.

Sai dai shugabannin ƙwadago sun dage cewa sai gwamnatin ta biya buƙatunsu, lamarin da bai kai su ga cimma matsaya ba.