✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’aikata ku tsaida harkokinku idan aka kama Ajaero – NLC

NLC ta ce za ta tsunduma yajin aikin da zai gurgunta al'amuran tattalin arziƙi a Najeriya.

Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC), ta umarci ma’aikatan ƙasar da su tsaida harkokinsu da zarar ’yan sanda, sun kama Shugaban Ƙungiyar, Kwamared Joe Ajaero.

Ƙungiyar, ta bayyana hakan ne, a matsayin martani ga gayyatar da ’yan sanda suka yi wa Ajaero kan zargin ɗaukar nauyin ta’addanci a Najeriya.

Hakan ne ya sa NLC ta kira taron gaggawa na Majalisar Zartaswa ta Ƙasa (NEC),  inda ta yanke shawarar rubuta wa ’yan sanda ƙarin wa’adi don bai wa ƙungiyar damar tuntuɓar lauyoyinta.

Da yake jawabi a taron gaggawar, mataimakin shugaban NLC, Kabiru Ado Sani, ya ce gayyatar Ajaero gayyata ce ga ma’aikata.

Ya ce, “A ƙarshen taron mun cimma wasu ƙudurori. Wani ɓangare na ƙudurin shi ne, a matsayin ƙungiyar ƙwadago, mun amince kuma mu masu bin doka da oda ne.

“Za mu mutunta gayyatar ’yan sandan Najeriya saboda mu ba ƙungiya ce mara alƙibla ba, amma muna buƙatar ƙarin lokaci, bayan tattaunawa da lauyoyinmu, domin an miƙa wa shugaban majalisar wannan gayyata ne, a jiya kuma aka nemi ya miƙa rahoto a ga ’yan sanda da ƙarfe 10 na safiyar Litinin.”

A gefe guda NLC ta ce matuƙar aka kama Ajaero, za ta tsunduma yajin aikin da zai gurgunta al’amuran tattalin arziƙi a Najeriya.