Daya daga cikin ma’aikatan lafiya dake aiki a Cibiyar Agajin Gaggawa ta Amurka ya kamu da Korona bayan an masa rigakafin maganin kamfanin Pzifer.
An dai yi wa ma’aikacin mai suna Matthew W. rigakafin kamfanin Pfizer da BioNTech, a ranar 18 ga Disambar 2020, inda a lokacin ya ce ba ya ji wani ciyo face na hannu.
- Kyauta za a yi wa ’yan Najeriya allurar rigakafin Coronavirus — PTF
- Iran ta fara gwajin rigakafin COVID-19 da ta samar a cikin gida
- Nan da watan Janairu Najeriya za ta shigo da rigakafin COVID-19 – Minista
- Tsohuwa mai shekara 90 ta fara amfani da rigakafin COVID-19 na Pfizer
Sai dai kafofin yada labarai dake kasar ta Amurka, sun bayyana cewa ya nuna wasu alamun cutar kwanaki shida bayan yi masa rigakafin.
Bayan masa gwaji kuma, sakamakon ya nuna yana dauke da cutar.
To sai dai masana bincike sun ce ba abun mamaki bane saboda bai nuna alamun da ake so ba lokacin da ya karbi rigakafin.
Wani likita dake Cibiyar Dakile Cututtuka ta San Diego a Amurka, Christian Ramers, ya ce ya kan dauki tsawon kwanaki 10 zuwa 14 kafin maganin ya fara aiki a jikin mutum.