✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Luka Modric na shirin hadewa da Ronaldo a Al-Nassr

Kungiyar ta Al-Nassr na shirin dauko dan wasan na Croatia.

Dan wasan tsakiya na kungiyar Real Madrid Luka Modric ya tafi Saudiya don tattaunawa da kungiyar Al-Nassr inda tsohon abokin wasansa Cristiano Ronaldo yake.

Wannan na zuwa ne gabanin yunkurin da ake na ganin dan wasan ya koma buga wasa a gasar Saudi Pro League.

Kungiyar ta Al-Nassr na shirin dauko dan wasan na Croatia, wanda ya koma Real Madrid daga Tottenham kan kudi Euro miliyan 35 a shekarar 2012.

Tun bayan komawarsa Madrid, dan wasan ya samu nasarar lashe kofuna 22 a kungiyar da kuma kyautar Ballon d’Or.