✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

LP ta lashe zaben Gwamna a Abiya

LP ta doke jam'iyyar PDP mai mulkin jihar

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana dan takarar LP, Alez Chioma Otti, a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan Jihar Abiya.

Hakan dai na nufin LP ta lashe Jiha ta farko, bayan ta kayar da jam’iyyar PDP mai mulkin Jihar a zaben da aka gudanar ranar Asabar.

A cewar jami’in INEC mai bayyana sakamakon zaben, Farfesa Nnenna Oti, dan takarar ya lashe zaben ne da kuri’a 175,467, inda ya doke babban abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP, Okey Ahiwe wanda ya sami kuri’a 88,529.

Kazalika, ya ce dan takarar YPP ne ya zo na uku da kuri’a 28,972, yayin da na APC ya zo na hudu da kuri’a 24,091.

Idan za a iya tunawa, hukumar INEC ta dakatar da ci gaba da tattara sakamakon zaben na Abiya daga Karamar Hukumar Obingwa, domin ta sake duba shi sakamakon zargin tafka magudi a can.