Alhaja Shareefaat Abiola Andu, furodusar fim din Turanci na Nollywood mai suna The Two Aishas na Rahama Sadau da Maryam Booth, ta ce lokaci ya yi da za a samar da ‘Mulliwood’ daga cikin Kannywood da kuma Nollywood.
Ga dalilinta da kuma yadda ta yi aiki da ’yan Kannywood a karon farko.
Yaya aka yi kika shiga harkar shirin fim la’akari da cewa da kayan sawa aka san kamfanin Arabel?
Watan Nuwamban wannan shekara za mu cika shekara 25 cif-cif in Sha’a Allah a harkar dinke-dinke da kayan sawa.
Yanzu na ga lokaci ya yi da za mu shiga a kuma dama da mu sakamakon yadda ake aron bakinmu Musulmai ana ci mana albasa ta hanyar yadda wasu ke bayar da labarinmu.
Mu mun san yadda muke, mun kuma san yadda ake fada game da mu ba haka ba ne.
Don ya haka ya kamata mu soma fada wa duniya labarinmu da kanmu don haka kuka na shiga harkar fim.
Gaskiya kishin Musulunci ne ya sa na shiga shirin fim.
A kamfanin Arabel duk abin da zai daga martabar Musulunci muna ciki.
‘The Two Aishas’ sh ine fim dinku na farko ke nan?
Eh, shi ne. Duk da cewa mun yi shirye-shiryen talabijin da yawa na Arabel, muna ma da lisisin talabijin mai suna ‘Alif TV’.
Amma a fim, wannan ne na farko, kuma na ga tunda muna da Kannywood da Nollywood da kuma Ghaliwood a Ghana, me zai sa ba za mu samu ‘Molliwood’ ba, na finafinan Musulunci da Musulmai?
Don haka sai na ce bari in saka dan-ba, da wannan Fim din. Ni dai ina son bayar da labarin Musulmai, ba kuma kawai bayar da labarin fim da Musulmai a ciki ba, bayar da labarin da ya dace.
Shin me ya sa ki ke son yin finafinan addini, la’akari da cewa muna da Musulmai (a Kannywod da Nollywood da kuma Ghaliwood, da ke wakiltar addinin?
A lokuta da yawa ina ganin labarai a finafainai masu kama da na Musulunci ko kuma Musulmai. Kamar yin salla a fim, ko sa hijabi wani irin abin dariya. Ni ba haka nake so in yi ba.
A nuna abin da ya kamata kuma yadda ya kamata. Ina da yadda zan yi da kuma gogewa da kwarewar da zan yi hakan (cikin yardar Allah).
Sannan a wani lokaci can baya, na taba halartar wani taron bikin baje kolin finafinai. Kuma a tattataunawar da ake yi a taron ana tattaunawa kan finafinan addini kuma tattaunawa ce da kwararru, sai na ga cikin masu tattaunawar wani Kirista ne.
Na dudduba duk cikin taron babu Musulmin da zai waklilci Musulunci, kuma a taro babba irin wanannan kuma na kasa.
Tun da haka sai na ce ‘lallai da sake’. Na kuma kudiri aniyar cewa sai na yi wani abu kan wannan lamarin.
Shi ne da na soma tunanin wannan fim din sai na samu wasu mutanen da muka tattauna, na kuma gabatar da rubutuna, bayan tattaunawa da kuma kai-komo na gyaran labari da saka duk abin da ya dace na zamani da kuma kyale-kyale sai na amince da labarin da a yi shi.
Kenan labarin kirkira ne ba ya faru da gaske bane ko?
Labarin kirkira ne dari bisa dari. Ni ma na sha tambayar cewa labarin wace ce?
Nakan ce, ba labarin kowa ba ne. Kikirarren labari ne kawai da ya samu rubutu mai kyau.
Bayan an rubuta shi na nuna wa wasu mutane, kuma sun bayar da ’yan shawarwarin da suka taimaka wa labarin matuka.
Shin yaya ki ka kai ga zabar Rahma Sadau da Maryam Booth su fito a cikin fim daga Kannywood, ta yaya aka yi wannan gamin gambizan da ’yan Nollywood?
A lokacin da na soma shirye-shirye na so in samu ’yan wasa Musulmai dari bisa dari daga Kudu da kuma Arewa. Sai na rika tambayar mutane su waye Musulmai cikin masana’antar?
Na dai san da yawa daga cikinsu na finafinan Yarbawa, don haka ina Musulmai Yarbawa ’yan Nollywood? Ban samu ba. Watakila ko don ba sa amsa sunan Abdulrashed ko Suleiman ko kuma Sherifatu ne.
Don haka ni ban san su ba. Ana haka ’yata Dija ta alkunya ta same da shawarar in sa Maryam Booth da Rahama Sadau, ta kuma tuntube su a madadina.
Da na ga ayyukan da suka yi, sai na naga lallai sun dace da rawar da nake so su taka a fim din, sai na yi magana da su, suka kuma amince cikin farin ciki, ba kuma su ba ni wata wahala ba.
Da kuma muka zo bangaren maza sai muka samu wadanda ba Musulmai ba, saboda ba mu samu Musulman ba daga Kudu, haka ma’aikata, shi ma na wahala samun Musulmai zalla.
Daga karshe na dau wannan mai bayar da umarnin, ba Musulmi ba ne, na kuma fada masa fim din Musulunci ne, ya ce babu komai aiki duk aiki ne, in dai za a sa shi a hanya. Haka kuma aka yi.
Ko yaya aikinki da Maryam Booth da Rahama Sadau ya kasance a lokacin daukar fim din, ko sun ba ki wata matsala?
Tun a ranar farko da muka yi magana da su a waya kafin mu hadu na ayyana a raina cewa mutanen kirki ne kuma ba zan samu matsala da su ba.
Hakan kuma aka yi. Domin sun bayar da cikakken hadin kai a yayin daukar shirin, sannan sun kuma bayar da abin da ake so a matsayin da suka fito na Aisha da Aisha.
Tun daga lokacin daukar shirin a watan Agusta zuwa Satumba (shekarar 2022) muke zumunci da tuntubar juna har yanzu bayan an gama.
Hakika na ji dadin aiki da su babu wata matsala da suka ba ni, musamman irin na nuna dagawa da fankama da aka san mayan jarumai.
Da fim din ya fito, sun tallata shi sosai a shafukansu na sada zumunta ba tare da neman ko kwabo ba.
Shin ki na ganin za ki sake aiki da ’yan Kannywood a nan gaba?
Kwarai kuwa, domin bayan wannan aikin fim na gwaji, abu na gaba shi ne wani aiki na hadin gwiwa tsakanin Kudanci da kuma Arewacin kasar nan ta wannan fuska, haka nake so in tafi da wannan tsari daga yanzu, domin farko shi ne Musuluncin da ya hada mu.
Aikin da zan yi nan gaba cikin yardar Allah zai zama wani gagagarumin hadin gwiwa ne da ya wuce daukar mutum biyu kawai daga Kannywood.