Lizz Truss ta Jam’iyyar Conservative, ita ce fira minista da wa’adinta ya fi gajarta a tarihin kasar Birtaniya.
Bayan kwana 44 a kan mulki, dambarwar siyasa da matsalolin siyasa suka sa ta ajiye aiki, kwanaki kadan bayana ta sallami ministan kudi kuma na hannun damanta, Kwasi Kwarteng.
- Ba a ba wa Matan karkara muhimmanci a gwamnati a Najeriya —MDD
- Amurka za ta ba mutanen da ambaliya ta shafa a Najeriya Dala miliyan daya
Ga muhimman abubuwan da suka faru a tsawon mulkin Liz Truss wanda rikici ya dabaibaye, har mambobin jam’iyyarta suka juya mata baya:
Ta fara aiki ne a ranar 6 ga Satumba, 2022 bayan dambarwar da ta yi sanadiyyar murabus din Fira Ministar Boris Johnson, wanda mulkinsa ke cike da rudani.
Kwananta 45 kacal a kan mulki, amma ta yi mulki tare da sarakunan Ingila biyu – sarki mai ci, Charless III da mahaifiyarsa, Sarauniya Elizabeth II, wadda ta fi kowa dadewa kan karagar mulki a kasar.
Hawan Liz Truss mulki da kwana biyu kacal, Sarauniya Elizabeth II ta rasu bayan shekara 75 tana mulki, sakamakon rashin lafiya.
Tsanantar rashin laifyar Sarauniya Elizabeth II da rasuwarta da kuma shirye-shiryen jana’iza sun dauke hankalin duniya daga abubunwa da suka faru a farkon wa’adin Misis Truss.
Ta hau mulki da zimmar tayar da komadar tattalin arzikin Birtaniya, wadda ke basuka suka yi wa katutu, amma matakan da ta dauka suka janyo raunin bangaren kasuwanci da kuma bakin jinni ga gwamnatinta.
Girgizar bangaren kasuwanci, karuwan bashi da faduwar darajar Fam sun tilasta mata janye karamin kasafinta mai cike da rudani, wanda ke shirin rage kudaden haraji da kara kudin ruwa.
A kimanin mako uku bayan shan suka daga ministocin jam’iyyarta, ta sallami ministan kudi, Kwasi Kwarteng, wanda na hannun damanta ne, ta maye gurbinsa Jeremy Hunt, tsohon makusancin dan adawarta.
Bankin Ingila ya kashe Fam biliyan 19.3 wajen saye takardun lamuni cikin gaggawa da nufin rage illar da tsarin Kwasi Kwateng ya haifar na faduwar hannayen jari da kuma barazana da ajiyar kudaden fansho.
Jaridar The Guardian ta Birtaniya ta ruwaito wani mai sharhi na cewa bakin jinin da kasafin ya janyo wa Liz Truss ya fi na Boris Jonhson da kashi 47%, a lokacin rikicin cikin gidan jam’iyyarsa.
Bayan kwana 44 a ofis, a ranar 20 ga watan Oktoba, 2022, ta yi murabus, saboda gazawar gwamnatinta na yin abubuwan da aka zabe ta ta yi.