Liverpool ta samu nasarar zuwa sawan karshe na Gasar Zakarun Turai bayan lallasa kungiyar kwallon kafa ta Villarreal da ci 3-2 har gida.
Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta samu wannan nasara ne bayan yin hobbasa daga ci 2 babu ko daya da Villarreal ta yi mata kafin tafiya hutun rabi lokaci.
- ‘Isra’ila na tsare da Falasdinawa kusan 600’
- UEFA ta dakatar da kungiyoyin Rasha daga gasar Zakarun Turai ta badi
Jim kadan bayan dawowa daga hutun rabin lokaci Liverpool ta warware kwallayen baki daya tare da kara wata a kai, wanda hakan ya ba ta nasarar samun tikitin zuwa wasan karshe na gasar.
Da farko dai Villarreal ta zura kwallo a minti na uku da fara wasan ta hannun dan wasanta Boulaye Dia, yayin da Francis Coquelin ya kara a minti na 41.
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Liverpool ta yi wasan kura da Villarreal, inda ’yan wasanta Fabinho, Luis Diaz da Sadio Mane suka jefa mata kwallaye a minti na 62 da 67 da kuma minti na 74.
Dama tuni Liverpool ta samu nasarar doke Villarreal da ci 2 babu ko daya a zagayen farko na wasan da aka doka a filin wasa na Anfield da ke kasar Birtaniya.
Kungiyar ta samu nasara da jimullar kwallaye 5 da 2 ke nan, wanda yanzu haka za ta jira kungiyar da za ta barje gumi da ita a wasan karshe na gasar tsakanin Real Madrid ko Manchester City, wadanda za su fafata a daren ranar Laraba.