Abun da za mu iya kawo muku ke nan a wannan wasa. Da fata kun ji dadin yadda muka kawo muku labarin wannan wasa kai tsaye. Sai gobe kuma inda za mu kawo muka wasan Real Madrid da Bayern Munich kai tsaye.
A gaskiya za a dade ba a samu wasa da ya yi zafi ba kamar wannan. Nasan hankulan masu kallo ya daga sosai tun daga farkon wasan har zuwa karshe. Sauram kallo sai a gidan Roma.
Alkalin wasa ya busa, kuma an tashi. Liverpool ta lallasa Roma da ci 5 da 2 a filin wasa na Anfield da ge kasar Ingila.
Salah ya ci 2, Firminho ya zura 2, sannan Mane ya zura 1 wa kungiyar Liverpool. Sanna Dzeko da Perotti wa kungiyar Roma.
A yadda aka tashi yanzu, Roma na neman akalla uku ke nan a gida, idan Liverpool ba ta zura kwallo ko daya ba.
90: An kara minti 4. Liverpool za ta yi canjin. Cin lokaci da wayau?
Saura minti daya a tashi. Roma na matsa Liverpool lamba
85: Goalllllllll.. Perotti ya zura kwallon daga kai sai mai tsaron gida. Liverpool 5 Roma 2
Penaltyyyyyyyyyyyyyyyyyyyyyyyyy: Roma ta samu bugun daga kai sai gola..
82: Goaaalllllllllllllllllllllllll: Dzeko ya zura kwallo daya. Liverpool 5 Roma 1. Roma ta share 0.
75: Ings ya canji Salah. Da alamu kocin Liverpool ya wadatu da kwallaye. Liverpool 5 Roma 0
68: Goallllllllllll… Firminho na zura kwallonsa na biyu. Liverpool 5 Roma 0. Da kamar wuya gaskiya. Roma ta sha bugu a gidan nan.
Roma ta yi canji biyu a tare: De Rossi ya fita inda M. Gonalons ya shigo, sannan Jesus ya fita inda M. Gonalons ya shigo
56: Goalllllllllll… Firminho.. Firminho ya zura kwallo na hudu. Shi ma Salah ne ya taimakasa. Salah ya ci biyu, ya taimaka sau biyu.
59: Har yanzu Liverpool 3 Roma 0
54: Goallllllllllllll… Mane ya zura kwallo na uku. Salah ya taimaka masa matuka wajen zura wannan kwallo
52: Wasa na kara zafi matuka. Roma sun fito suna neman kwallo. Suma Liverpool sun kara dagewa suna neman kari. Liverpool 2 Roma 0
Yanzu haka an dawo filin daga. Ko Roma za ta farke? ko kuma Liverpool za ta kara? Za mu gani a nan da minti 45 da ‘yan kari.
An je hutun rabin lokaci. Liverpool 2 Roma 0. Salah ne ya zuk kwallon guda biyu.
45: An kara minti biyu.
44: Goalllllllllllllllllll.. Salahhhhhh… Salah ya zura na biyu. Liverpool 2 Roma 0. Salah na lokaci gaskiya. Ya zura kwallon biyu. Yanzu haka yana da kwallon na 10 ke nan.
43: Har yanzu Liverpool 1 Roma 0
Firminhooooo.. Ayya saura kiris.
Liverpool na neman kwallo na biyu cikin sauri. Suna kara matsa wa Roma lamba.
Liverpoollllllllllllllllll… Ayya. Liverpool ta kara.. Ayya kwallon ta bugi sandan fos.
35: Goalllllllll………. Salah ya zura wa Roma kwallon farko.. Liverpool 1 Roma 0.
Goallllllllllllllllllllllllllll… Mane ya zura kwallon farko a ragar Roma.. Ayyaaaaa… Ashe ya yi satar gida. Rafare ya hura. Har yanzu canjarasa. Babu ci
31: Har yanzu babu ci, amma Liverpool na neman zura kwallo ruwa a jalo.
Salahhh…. Golan Roma ya cire. Wasa fa na kara zafi. Liverpool sun matsa wa Roma lamba.
Saura kiris.. Mane ya samu dama guda biyu a jere a cikin minti daya, amma duka ba sa’a. Kwallon ta ki shiga.. Kash! wannan dai rashin sa’a ne.
27: Har yanzu babu ci.
Mane ya dauka da gudu. Ayya Juan Jesus ya maka shi da kasa. An ba Jesus kafin gargadi.
Minti 23: Har yanzu canjaras.. Babu ci. Amma fa ana taka leda
Wijnaldum ne ya canji Chamberlain saboda raunin da ya samu.
Goalll… ayyyaaaaa… kwallpn ya buga sandar fos ya fita.. Kash.. Kolarov ya tayar wa Liverpool da masoyansu hankali. Irin wannan duma haka?
Saura kiris.. Roma ta kusa, ayya…
17: Chamberlain ya ji rauni bayan ya yi kokarin kwace kwallo a wajen dan Roma. Da alama raunin mai karfi ne domin za a canja ne baki daya. Kash! kuma gasar cin kofin na karatowa.
13: Roma ta kai hari. Inda aka dago kwallon sama domin Ddzeko ya samu, amma mai tsaron gidan Liverpool Karius ya yi kusa. Ya dauke kwallon a sama.
Minti 7: Chamberlain ya yi duma daga nesa, amma golan ya kama cikin sauki. Ana ta tirkatirka dai har yanzu, amma babu ci.
An canja ma mataimakin rafare tuta bayan wanda ke hannunsa ya karye. An taba samun haka a tarihin kwallo kuwa?
Saura kiris: Firminho ya barar da wata dama mai kyau. Saura kiris ya zura kwallon. Assha.. ina ma ace Salah ne.
An fara taka leda yanzu haka. Kuma da alamu dukan bangarorin sun fito neman kwallo ne. Kowa ya kai hari daya. Strootman ya kai harin gidan Liveropool, yayin da shi ma Salah ya kai harin gidan Roma
‘Yan wasa: Liverpool (4-3-3): Karius; Alexander-Arnold, Lovren, Van Dijk, Robertson; Oxlade-Chamberlain, Henderson, Milner; Salah, Firmino, Mane.
‘Yan benchi: Clone, Wijnaldum, Klavan, Moreno, Mignolet, Ings, Solanke
Roma (3-4-2-1): Alisson; Fazio, Manolas, Juan Jesus; Florenzi, De Rossi, Strootman, Kolarov; Under, Nainggolan; Dzeko.
‘Yan benchi: Pellegrini, Perotti, Schick, Gonalons, Bruno Peres, Skorupski, El Shaarawy.
A yau ne za kece raini tsakanin kungiyar Liverpoll da Roma a filin wasa na Anfield a bugun kusa da karshe.
Mohammad Salah na yin lokaci kuma kungiyarsa ta Liverpool na kokari matuka musamman a gasar zakarun Turai. Haka ita ma Roma tana kokari musamman ganin yadda ta yi waje da kungiyar Barcelo da kafin wanan wasar, ba a samu kungiyar da ta doke tab a.
Masu sharhi dai suna ganin kamar Roma kanwar lasa ce, don haka suke tunanin Liverpool za ta yi waje da ita, amma kuma suna ganin ai sai an buga kawai.
Ku biyo anjima kadan, inda za mu kawo labarin yadda wasan ke wakana kai tsaya.