Liverpool ta maimaita tarihin cin kwallaye da tazara mai yawa bayan ta lallasa Bournemouth da ci 9-0 a wasan mako na hudu a gasar Firimiyar Ingila da suka kara a Anfield ranar Asabar.
Ragowar lokuta ukun da suka faru a tarihi sun hada da wasan da Manchester United ta yi wa Southampton 9-0 a shekarar 2021. Sai wanda Leicester City ta ci Southampton 9-0 a 2019.
- An kori sojojin da ake zargi da kisan Sheikh Aisami daga aiki
- Muna asarar miliyoyin Naira duk mako —Dillalan Shanu
Haka kuma, a shekarar 1995 ce Manchester United ta lallasa Ipswich Town 9-0 a Firimiyar ta Ingila.
Karon farko dai ke nan Liverpool ta zazzaga kwallo tara a raga a wasa a Firimiyar Ingila tun bayan da ta taba cin Crystal Palace 9-0 a shekarar 1989.
Haka kuma a karon farko ke nan da kociyan kungiyar, Jurgen Klopp ya ci kwallo tara a wasa daya a tarihin sana’arsa ta horar da tamaula.
Minti uku da soma wasan Liverpool ta fara zura kwallo ta hannun Luis Diaz daga baya Harvey Elliott ya kara na biyu a minti uku tsakani.
Karon farko da Liverpool ta ci kwallo biyu a raga cikin minti shida a Firimiyar tun bayan Maris din shekarar 1996 da ta yi wa Aston Villa haka.
Roberto Firminho ne ya bayar da dukkan kwallayen biyu da aka zura a raga cikin minti shidan, ya zama na biyu a wannan bajintar a Firimiyar tun bayan Islam Slimani a Disambar 2016 a wasan Leicester da Man City.
Trent Alexander-Arnold ya kara na uku a ragar Bournemouth kuma Firminho ne ya bashi kwalon, sannan dan wasan Brazil din ya zura na hudu tun kan hutu.
Virgil van Dijk ne ya ci na hudu, minti daya tsakani Chris Mepham ya ci gida, sai Roberto Firmino ya kara na biyu a wasan kuma na bakwai da Liverpool ta ci.
Kungiyar Anfield ta zura na takwas a raga ta hannun Fabio Carvalho, sannan Luis Diaz ya ci na tara a wasan.
Kwallon da Liverpool ta sharara da yawa a raga a Firimiyar har da cin Rotherham Town 10-1 a shekarar 1896.
Liverpool ta soma Firimiyar bana da canjaras 2-2 a gidan Fulham a gasar ta bana, sannan ta yi 1-1 a Anfield da Crystal Palace ta kuma yi rashin nasara da ci 2-1 a hannun Manchester City.
Ranar 31 ga watan Agusta Liverpool za ta karbi bakuncin Newcastle United a wasa na biyar a Firimiyar Ingila.