✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Liverpool da Brighton sun haska tauraruwarsu a Gasar Europa

Brighton ta samu nasara ta farko a tarihinta a gasar.

Ƙungiyar ƙwallon kafa ta Liverpool da takwararta Brighton and Hove Albion, sun haska tauraruwarsu a Gasar Kofin Europa ta bana da ke ci gaba da wakana a Turai.

Liverpool dai ta ci gaba da taka rawar gani a gasar cin kofin Europa bayan da ta doke kungiyar Toulouse ta Faransa da ci 5-1 a rukunin E.

Masu masaukin baki sun fara jefa kwallo a raga a filin wasa na Anfield ta hannun Diogo Jota a minti na tara da fara wasa.

Toulouse ta mayar da martani ta hannun Thijs Dallinga, amma Wataru Endo da Darwin Nunez sun ci wa Liverpool kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Ryan Gravenberch ya ci wa Liverpool kwallo na hudu kafin Mohammed Salah wanda ya shigo daga baya ya karasa, inda ya ci a cikin karin lokaci.

Nasarar na nufin Liverpool ta tabbatar da matsayinta a saman rukunin E, da maki tara bayan wasanni uku, yayin da Toulouse ta tsaya ta biyu da maki hudu.

Ita kuwa Brighton ta samu nasara ta farko a tarihinta a gasar, inda ta doke Ajax da cin 2-0 a yunkurinta na ketarawa zuwa zagaye na gaba.

Yanzu Brighton tana mataki na uku a rukunin B, maki daya a bayan Marseille da ke jan ragamar rukunin da maki biyar.