✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Amurka ta yi fatali da ƙudirin janye dakarun ƙasar daga Nijar

Shin akwai hikima a bar dakaru sama da 1,000 a kasar da sojoji suka yi juyin mulki?

Majalisar Dattawan Amurka ta yi fatali da wani kuduri da zai bukaci Shugaba Joe Biden ya janye dakarunsu daga Jamhuriyar Nijar bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Yuli.

A kuri’ar da suka kada a kan kudurin, ’yan majalisa 86 sun yi watsi da shi yayin da 11 suka amince da shi.

A watan nan ne Amurka ta bayyana a hukumance cewa an yi juyin mulki a Nijar, abin da ya sa ta daina bai wa kasar tallafi kamar yadda dokarta ta ce.

Sai dai wasu daga jami’an gwamnati sun ce ba a bukatar janye dakarun kasar daga Jamhuriyar Nijar.

Amurka ta dade da kulla yarjejeniyar tsaro da Nijar inda suke yaki da ’yan ta’adda da ke da alaka da kungiyar Al Qaeda da ISIS a yankin Sahel.

A halin yanzu akwai kimanin dakarun Amurka 1,000 da ke aikin kakkabe ’yan ta’adda a kasar ta Jamhuriyar Nijar.

Sanata na jam’iyyar Republican, Rand Paul, wanda ya dauka nauyin kudurin, ya dage cewa ba a bi ka’ida ba wajen aika sojojinsu Jamhuriyar Nijar.

A cewarsa, majalisar dokoki ba ta amince da matakin ba tun da farko abin da ke jefa dakarun kasar cikin hatsari.

“Tun da yanzu ana rikici a Gabas ta Tsakiya, wacce hujja muke da ita ta barin dakaru fiye da 1,000 a Nijar?

“Shin akwai hikima a bar dakaru sama da 1,000 a kasar da sojoji suka yi juyin mulki?” kamar yadda Sanata Paul ya bayyana a jawabin da ya gabatar a zauren majalisar dattawan.

Sai dai Sanata Ben Cardin na jam’iyyar Democrat kuma shugaban kwamitin harkokin kasashen waje na majalisar, ya ce za a samu gagarumin gibi a yankin Sahel idan aka janye dakarun kasar daga Nijar.

Ya bayyana cewa janye dakarun zai bai wa Rasha da kungiyar sojojin haya ta Wagner damar cin karensu babu babbaka a yankin.

“Ba ma mayar da hankali sosai a wannan yankin na duniya. Don haka bai kamata mu nuna alamun cewa mun yi watsi da lamuran yankin ba,” in ji Cardin.

Tuni dai Faransa, wadda ta yi wa Nijar mulkin-mallaka, ta soma janye dakarunta fiye da 1,500 daga Jamhuriyar Nijar bayan dangantaka ta yi tsami a tsakaninsu sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi wa Mohamed Bazoum.