✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Liverpool da Arsenal sun yi kunnen doki a Anfield

Karon farko da Arsenal ta ci Liverpool kwallo biyu a Anfield a Firimiyar Ingila tun Satumbar 2012.

Liverpool da Arsenal sun tashi 2-2 a wasan mako na 30 a gasar Firimiyar Ingila da suka buga ranar Lahadi a Anfield.

Minti takwas da fara wasa Arsenal ta ci kwallo ta hannun Gabriel Martinelli, kuma minti 20 tsakani Gabriel Jesus ya kara na biyu.

Kwallon da Martinelli ya ci na 25 a Premier League kenan, ya zama na biyu daga Kudancin Amurka, bayan Gabriel Jesus da ya yi wannan bajinta masu shekara 21 da haihuwa.

Karon farko da Arsenal ta ci Liverpool kwallo biyu a Anfield a Firimiyar Ingila tun Satumbar 2012 a karawar da Gunners ta yi nasara da ci 2-0.

Saura minti uku su je hutu ne Mohammed Salah ya zare daya, daga baya Roberto Firmino ya farke saura minti uku a tashi, wanda ya shiga karawar daga baya.

Ba wani dan wasa da ya ci Arsenal kwallo da yawa ba a bugun fenariti a ciki kamar Firmino mai 10 a raga.

Da wannan sakamakon Arsenal ta ci gaba da zama ta daya a kan teburin Premier da maki 73, Liverpool mai kwantan wasa tana ta takwas da maki 44.

Saura maki shida yanzu tsakanin Gunners da Manchester City ta biyu mai kwantan wasa mai maki 67.

Ranar Lahadi 16 ga watan Afirilu, Arsenal za ta ziyarci West Ham, domin buga wasan hamayya a karawar mako na 21 a Firimiyar.

Leeds United za ta karbi bakuncin Liverpool ranar Litinin 17 ga watan Afirilu a Elland Road.