✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Littafin Tarbiyyar Yara A Musulunci A Mahangar Sharhi

Sunan Littafi: Tarbiyyar Yara A Musulunci Sunan Marubuciya: Maimunatu Abba WabiKamfanin dab’i: Hamida Printing Press Limited AzareYawan Shafuka: 66Shekarar Wallafa: 2014Farashi: Ba a fada ba…

Sunan Littafi: Tarbiyyar Yara A Musulunci

Sunan Marubuciya: Maimunatu Abba Wabi
Kamfanin dab’i: Hamida Printing Press Limited Azare
Yawan Shafuka: 66
Shekarar Wallafa: 2014
Farashi: Ba a fada ba

Addinin Musulunci dai cikakken addini ne da ya kunshi rayuwa dukkanta. Allah Ya halicci dan Adam domin ya rayu a doron kasa a matsayin halifanSa. Bai sauko shi ba sai da Ya turo masa da shiriya da ka’idojin yadda zai rayu ta hannun manzanninSa masu tsarki. Ke nan ya wajaba ga mutum ya nemi ilimi da tarbiyyar yadda zai gudanar da rayuwarsa kamar yadda Allah Ya shar’anta masa.
Ga duk mai son bayar da ingantattar tarbiyya ga ’yara, littafin Tarbiyyar Yara A Musulunci shi ne abokinsa, domin kuwa an fayyace dalla-dalla, matakai-matakai yadda za a kimsa wa yara tarbiyya a musulunce. Mafi yawan matsalolin rayuwa da muke fuskanta a wannan zamani, sun samo asali ne sanadiyar rushewar tarbiyya. Kamar yadda marubuciyar littafin ta fada a gabatarwa: “Shin ko muna nazari don mu gano dalilan da suka jefa mu a cikin wannan yanayi na tsaka mai wuya kuwa? To ba wani abu ba ne illa watsi da muka yi da tarbiyyar da Allah Ya tsara mana, muka kauce wa koyarwar Musulunci, muka je muna bin ’yan kame-kame, wadanda sam ba su da alkibla guda daya a rayuwa. Idan kuwa har muka ci gaba da wannan lalube a cikin duhu, to a haka rayuwarmu za ta yi ta tafiya cikin rashin jin dadi da rashin samun natsuwa a cikin zuciya har ’ya’ya da jikokinmu. Allah Ya kiyaye.” (Shafi na bii).
An tsara littafin nan cikin saukakakken harshe, bisa tsari mai dacewa tare da zayyana kanun bayanai, sannnan bayanin ya biyo baya. kunshiyar littafin ta faro ne daga shafi na 1 zuwa na 8, inda aka yi bayani game da hakkokin yara a Musulunci. Daga nan kuma daga shafi na 9 zuwa na 11 aka yi bayani dalla-dalla dangane da manufar addinin Musulunci game da tarbiyyar ita kanta.
Kamar yadda bayani ya gabata, cewa Allah Ya saukar da littattafan shiriya ga al’umma ta hannun annabawanSa, to ta haka, daga shafi na 12 zuwa na 18, marubuciyar nan ta zayyano wasu ayoyin Alkur’ani Mai Girma, wadanda suka yi bayani game da ’ya’ya da tarbiyyarsu, ma’ana yadda za a bi da su domin su samu shiriya a rayuwarsu.
Shi kansa manzon Allah, Muhammadu (SAW), ya kasance babban malami, wanda ya shiryar da al’umma. Dangane da haka, daga shafi na 19 zuwa na 22, marubuciyar nan ta kalato wasu kadan daga cikin bayanan yadda Annabi Muhammadu (SAW) ya koyar da tarbiyya. Daga shafi na 23 zuwa na 39 kuwa, sai littafin ya yi tariya da bayanin tarbiyya a mahangar malaman tarbiyya.
A wajen tarbiyya, ita kanta halayyar yara da canjawarta abar kulawa ce a yayin da ake bayar da tarbiyya. Dalili ke nan marubuciyar nan ta sadaukar da shafi na 40 zuwa na 42 wajen bayyana yadda halayyar yara take idan suka fara ganin canji a jikinsu. Haka kuma su kansu masu ba da tarbiyyar, akwai dabi’un da suka kamata su mallaka da kuma matakan da suka kamata su bi. Dalili ke nan ya sanya tun daga shafi na 43 zuwa 56, marubuciyar ta yi bayani dalla-dalla game da masu ba da tarbiyya, bangarorin tarbiyya da kuma siffofin mai ba da tarbiyya.
Daga shafi na 57 zuwa na 62, an yi bayani game da abubuwan da ke bata tarbiyya da yadda za a gyara. Sai kuma shafi na 63 zuwa na 64, inda aka yi bayani gamsasshe game da tsarin tarbiyya. A yayin da kuma a shafi na 65 aka bayyana sunayen littattafan da marubuciyar ta gudanar da bincike a cikinsu.
Babu shakka littafin nan ya zo a kan kari kuma an yi amfani da amsasshiyar Hausa wajen rubuta shi. An samu bayyanar ’yan kura-kurai nan da can a cikin littafin, wadanda ba su taka kara sun karya ba, wadanda mafi yawansu ma na tuntuben na’ura ne. Haka kuma, zayyanar da aka yi a bangon littafin ba ta dace da littafin ba. Maimakon a yi zayyana mai kyau da hoton da ya dace sai aka shiga kwamfuta aka dauko wani karamin hoto aka lika a bangon. Ya dace a kula da wadannan kura-kurai, a gyara su a lokacin da aka zo sake gurza littafin.
Ya dace iyayen yara da cibiyoyin ilimi da dakunan karatu su tanadi littafin nan, domin kuwa babban rumbu ne da ke kunshe da ilimi da hikimomin koya tarbiyya ga yara da ma al’umma baki daya.