✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Littafin Dokta Al-Khudairi zai gyara tauhidin al’ummar duniya

Sunan Littafi: Tambaya Da Amsa Dangane Da Tauhidi Sunan Marubuci: Dokta Ibrahim Al-KhudhairiFassarar Ingilishi: Mahmoud Ridha MuradYawan Shafuka: 115Kamfanin Wallafa: Murad Applications, Riyad Saudi Arebiyadaukar…

Sunan Littafi: Tambaya Da Amsa Dangane Da Tauhidi

Sunan Marubuci: Dokta Ibrahim Al-Khudhairi
Fassarar Ingilishi: Mahmoud Ridha Murad
Yawan Shafuka: 115
Kamfanin Wallafa: Murad Applications, Riyad Saudi Arebiya
daukar Nauyi: Sashen Addinin Musulunci, Ma’aikatar Hulda Da Jama’a, Riyad, Saudi Arebiya.

kishirwar da mutane suke da ita kan ilimin akida, musamman abin da ya shafi tauhidi, dangane da kadaita Allah a matsayin abin bauta Shi kadai da kore masa kishiya; shi ya sa shehin malami Dokta Ibrahim Al-Khudairi ya wallafa littafi wanda ya sanya masa suna Tambaya Da Amsa Dangane Da Tauhidi. Ya zama dole a jinjina wa mawallafin littafin bisa la’akari da jajircewar da ya yi wajen bayar da gudunmawarsa daga ilimin da Allah Ya sanar da shi, ya fadakar da al’ummar Musulmi tsantsar tauhidi. Shi ma wanda ya fassara littafin daga harshen Larabci zuwa harshen Turanci, shi ma ya cancanci yabo saboda kokarin da ya yi na yi wa littafin fassarar da ta dace duk da irin bambancin da ke tsakanin harsunan guda biyu ta fannin furuci da ma’anonin kalmomi. Har ma yana cewa a shafi na daya na littafin: “Na gode wa Allah da Ya ba ni damar fassara wannan littafin daga Larabci zuwa Turanci don fadakar da ’yan uwa Musulmi, wadanda ba su jin harshen Larabci. Sau da dama na yi amfani da fassara mai ’yanci a maimakon fassarar kai-tsaye ko kuma fassarar kalma zuwa kalma, don na saukaka wa mai karatu gane abin da littafin ya kunsa. Domin yi wa kalmar Labaraci fassarar kalma zuwa kalma yakan jirkita ma’ana, shi ya sa sai na karanta Larabcin na fahimci abin da mawallafin yake nufi sannan sai na fassara abin da na fahimta.”
Babu shakka littafin ya burge sosai idan aka yi la’akari da yadda aka tsara shi bisa tambaya da amsa. Hakan shi zai ba mai karatu saukin fahimtar sakon da ake so a isar masa ba tare da wata mushkila ba.
Misali, a shafi na biyar an fara da me ye dalilin da ya sa Allah Ya halicce mu? Me ake nufi da Shari’a kuma mene ne rukunonin Shari’a? Abubuwa guda hudu da ya kamata kowane Musulmi ya sani. Haka tsarin littafin ya tafi har zuwa karshe.
Wani abu da zai ja hankalin mai karatu shi ne yadda aka yi wa littafin kyakkyawan bugu tare da bin tsari da ka’ida ta rubutu kuma babu shakka wadanda suka duba littafin sun yi masa gyaran kwakwaf, ta yadda da wahala mai karatu ya ga kura-kurai masu yawa. Gaba daya za mu iya cewa babu yadda za a kushe kyawun bugun littafin da kuma ingancin na’urar da aka yi amafani da ita wajen buga shi.
Dadin-dadawa, sunan littafin ya dace da jigonsa kuma mai karatu ba sai ya sha wahala ba zai gane ainihin sakon da ake so a isar masa ba tare da bata lokaci ba saboda yadda aka tsara littafin da sigar tambaya da amsa. Wani abin burgewa ma shi ne yadda mawallafin littafin ya rika bayar da bayanai dalla-dalla tare da fadin ayoyi da hadisai da maganganun malamai magabata a karshen kowane shafi na littafin, ta yadda idan mai karatu yana so ya bincika hujjojin da ya bayar ba sai ya sha wahala ba, zai ga inda ya samo hujjojin da sunayen littattafan da ya yi nazari nan take. Misali, a shafi na 13 ya ce ya samo hujjojinsa ne daga sura ta 58 aya ta 22 da sura ta 4 aya ta 36 inda yake bayanin abubuwan da Allah Ya fi tsana da wadanda Ya fi so. Ya ce abin da Allah Ya fi so shi ne a kadaita Shi, abin da kuma Ya fi ki ita ce shirka.
Baki daya za mu iya cewa littafin ya amsa sunansa kuma sakon da ake so a isar ga jama’a, babu shakka zai kai ga duk wanda ya karanta littafin ba tare da wata matsala ba. Hakazalika, mawallafin ya bayyana cewa abubuwan da ya fada a cikin littafin wani bangare ne na tauhidi don dalibai na matakin farko. Kuma ya nemi Allah Ya cika masa burinsa na ilimantar da jama’a tare da samun lada mai yawa.