✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Littafin Bin Baz ya raba takaddama kan tawassuli da neman tabarruki

Sunana Littafi: Bayanai A Kan Neman Albarka Da Neman Kamun kafa Da Hukuncin kwallafa kai A kaburbura. Marubuci: Shaik Abdul-Aziz Ibn Abdullah Bin BazFassara: Ba…

Sunana Littafi: Bayanai A Kan Neman Albarka Da Neman Kamun kafa Da Hukuncin kwallafa kai A kaburbura.

Marubuci: Shaik Abdul-Aziz Ibn Abdullah Bin Baz
Fassara: Ba a bayyana ba
Shafuka: 30

Martanin da babban malamin nan dan kasar Saudiyya mai suna Shaik Bn Abdul’aziz Ibn Abdullahi bn Baz ya yi wa hamshakin malami nan mai suna Muhammad Wa’iz Zaadak Alkhurasani, kan batun neman kamun kafa da neman albarka a Musulunci ya kayatar sosai.
Saboda Shaik Bn Baz a cikin littafinsa mai suna Majmu’ul Fatawa, mujalladi na tara a shafi na 105 wanda aka mayar da shi dan karamin littafi da aka fassara da harshen Hausa aka sanya masa suna: Bayanai A Kan Neman Albarka Da Neman Kamun kafa Da Hukuncin kwallafa Rai A kaburbura, ya yi amfani da hikima da fasaha wajen mayar da martani ga malamin ba tare da bakaken maganganu da kuma miyagun kalmomi ba.
Abin da zai burge mai karatu a cikin littafin shi ne yadda Shaik Bn Baz ya fara da yin addu’a ga kansa da malamin gaba daya, inda yake cewa a shafi na uku: “Allah Ya ba ni fahimtar addini da kai gaba dayanmu kuma Ya tseratar da mu daga barin hanyar wadanda aka yi fushi da su, Amin.”
Wani abin da zai kayatar da mai karatun littafin shi ne, yadda Shaik Bn Baz ya rika yin amfani da kalmomin jan hankali tare da tausasa harshe da yaba wa kokarin malamin da yake yi wa raddi, inda yake cewa a shafi na uku: “Hakika littafinku ya same ni, Allah Ya sadar da ku da igiyar shiriya da dacewa.” Ya ci gaba da fadin cewa: “Hakika a cikin littafin naku akwai al’amuran da suke bukatar bayani da karin haske da gusar da abin da kuka fada a cikinsa na shubuha.”
Wani darasi da malamanmu ya kamata su koya dangane da littafin shi ne, yadda Bin Baz ya warware kullin da malamin ya yi a cikin littafinsa ba tare da tayar da jijiyar wuya ko fadar bakar magana ko cin mutunci ba. Misali, tun daga shafi na hudu zuwa na bakwai ya kawo maganganun malamin, inda malamin ya nuna cewa ya halarta mutum ya yi tawassili da Annabi ko da wani salihin bawa kuma ya halatta mutum ya nemi tabbaruki da kabarin Annabi ko bango ko kofofin masallacin Annabi da na harami; inda Shaik Alkhurasani ya kafa hujja da wasu hadisai da suka nuna wadansu sahabbai sun yi tabbaruki da guraben Annabi bayan rasuwarsa. Misali, inda ya kawo cewa an samu Abdullahi dan Umar yana shafar minbarin Annabi don neman tabbaruki.
Shaik Alkhurasani ya kafa hujja da cewa sahabbai da suke neman albarkar gashin Annabi da guminsa da tufafinsa da sauransu da kuma hujjar da ya kafa cewa wasu sahabbai sun rika yin tawassuli da wasu sahabbai don yin addu’a ta musamman kamar lokacin da aka nemi Sayyidina Abbas ya yi addu’a don a samu ruwan sama da makamantansu.
To, amma Shaik Bn Baz da ya tashi mayar masa da martani sai ya kasa mas’alar gida biyu, don ya saukaka wa masu karatu fahimtar batun cikin sauki ba tare da sun sha wuya ba. Misali na a cikin shafi na bakwai, sai ya ce: “Na farko, yin tabbaruki da abin da ya shafi jikin Annabi na daga ruwan alwala ko gumi ko gashi ko kwatankwacinsu, ya ce halattacce ne a wurin sahabbai da wadanda suka biyo bayansu da kyautatawa amma a shafi na tara sai ya ce shafar bango ko kofofi ko tagogi masallaci mai alfarma na Ka’aba ko masallacin Annabi bidi’a ce, ba shi da asali a addini.”
Bin Baz ya ci gaba da cewa a shafi na tara: ‘Abin da ya wajaba a kan Musulmi shi ne ya takaita ga abin da Allah Ya shara’anta masa kamar dakumar bakin dutse da sumbartarsa da dakumar kusurwar da take kafin kusurwar bakin dutse na Ka’aba. Hakazalika Bn Baz ya ce hujjar da Shaik Alkhurasani ya kafa ta abin da Abdullahi dan Umar ya aikata, mahaifinsa da sauran sahabbai ba su yi muwafaka da shi ba a kan hakan, duk da cewa sun fi shi sanin al’amarin.
Bn Baz ya ce a shafi na goma: “Rokon annabawa da waliyyai da neman agaji a wurinsu da yin bakance saboda su shirka ce. Irin haka kafiran kuraishawa suka yi da gumakansu.”
Duk da cewa littafin ya tsaru kuma an yi masa bugu mai kyau, akwai kura-kuran dab’i da na ka’idajojin rubutu da yawa. Misali, a bangon littafin wanda ya fassara shi ya yi kuskuren hada kalmar ‘akan’ a maimakon ‘a kan’ da hade kalmar ‘dashi’ a maimakon ya raba ‘da shi’ da hada kalmar ‘yayi’ a maimakon ‘ya yi.’ A shafi na 28, ya hade kalmar ‘shine’ a maimakon ‘shi ne.’
Wanda ya fassara littafin ya yi kokari matuka gaya wajen yin fassara mai ’yanci a wurare daban-daban tare da yin fassara kai tsaya a wurare masu yawa.