Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Litinin 14 ga Yuni, 2021 a matsayin hutu domin zagayowar Ranar Dimokuradiyya, wadda za a yi bikin ranar Asabar 12 ga watan.
Sanarwar hutun ta bukaci ’yan Najeriya su kyamaci duk wani yunkurin raba kasar, su kuma mara wa gwamnati baya wajen wanzar da zaman lafiya da cigaban kasar.
- Da a biya kudin fansa gara ’yan bindiga sun kashe ni —Matar El-Rufai
- Matsalar Tsaro a Arewa maso Yamma ta kai ni bango — Buhari
Sakon na Minisatan Harkokin Cikin, Rauf Aregbesola, ya ce, “A yayin a muke bikin zagayowar Ranar Dimokuradiyya, mu tuna da namijin kokarin magabatanmu na tabbatar da Najeriya a matsayin kasa daya dunkulalliya.
“Matsalolin da suka dabaibaye ta a yanzu dama ce gare mu na watsewa ko dunkulewa; mu fada wa kawunanmu gaskiya ta yadda za mu mutunta juna mu fahimci juna domin mu zauna tare cikin aminci,” inji sakon na Aregbesola.
Sanarwar hutun da kakakin Ma’aikatar, Shuaib Belgore, ya fitar ta ba wa ’yan Najeriya tabbaci cewa Shugaba Buhari na yin abin da ya dace domin tsare dukiyoyi da rayuka, bunkasa tattalin arziki da kuma daidaita kasar.
Idan ba a manta ba, shekara biyu da suka wuce ne Gwamnatin Tarayya ta mayar da bikin Ranar Dimokuradiyya 12 ga watan Yuni, sabanin 29 ga watan Mayu da aka shafe shekara 19 a hakan.
Bikin na bana ya kama ne a ranar Asabar, wanda ya sa aka ayyana Litinin a matsayin ranar hutu.