Kamfanin Mai na Kasa (NNPC), ya sake jadadda wa ’yan Najeriya cewar matsalar karancin mai da ake fama da ita za ta kare nan ba da jimawa ba a daidai lokacin da take sa ran shigo da lita biliyan biyu da miliyan 300.
Babban Daraktan kamfanin, Adetunji Adeyemi ne, ya bayar da tabbacin a Abuja lokacin da yake jawabi dangane da yunkurin da kamfanin yake yi na samun isasshen mai, bayan shigo da gurbataccen mai da aka yi sati biyu da suka gabata.
- Rikicin APC a Kano: A shirye muke mu shirya da su Shekarau — Ganduje
- ’Yan bindiga sun aure 13 cikin daliban FGC Yauri da suka sace
Mista Adeyemi, ya bayyana cewar NNPC na sa ran shigowar lita biliyan 2.3 na man fetur zuwa Najeriya zuwa karshen watan Fabrairu, yayin da kuma tuni kamfanin ya raba lita biliyan daya a sassan kasar nan don rage karacin mai da ake fama da shi.
Kazalika, ya bayar da tabbacin cewar an rarraba man fetur zuwa gidajen mai da ke fadin kasar nan, kuma komai zai koma daidai nan da zuwa karshen watan da mu ke ciki.
Adeyemi ya ce NNPC ya bai wa gidajen mai umarnin raba man fetur yadda ya dace ga ’yan Najeriya cikin sa’o’i 24 masu zuwa.
Sannan ya kara da cewar kamfanin, zai baza komarsa don tabbatar da cewar man ya isa duk inda ya dace, a fadin kasar nan.