Gwamnatin Jihar Borno ta bukaci taimakon Kasar Saudiyya a fannin inganta ilimin addini da na harshen Larabci da ma abin da ya shafi tsaro.
Gwamna Babagana Zulum ne ya gabatar da bukatar lokacin da Farfesa Hassan Abdulhamid Bukhari, wanda mashahurin malami ne kuma guda cikin Limaman da ke jan sallah a Masallacin Harami na Makkah, ya ziyarci gwamnan a Maiduguri.
Zulum ya kuma bukaci taimakon Saudiyyar ta fuskar yaki da tsattsauran ra’ayi a yunkurin wanzar da zaman lafiya a Jihar ta Borno.
Imam Bukhari, wanda shi ne Shugaban Tsangayar nazarin harshen Larabci ga ajamawa a Jami’ar Ummul Qura da ke Makkah, ya ziyarci Maiduguri bisa gayyatar Dokta Mohammed Kyari Dikwa, Shugaban Gidauniyar Al-ansar wacce a halin yanzu ke gina jami’a mai zaman kanta ta farko a Maiduguri.
Limaman Masallacin Ka’aban, a yayin ziyarar ya bayyana farin cikinsa kan kyakkyawar tarbar da ya samu a Jihar Borno mai tsohon tarin makaranta Alkur’ani.
Ya ce jihar ta shahara da gwanayen makaranta Alkur’ani mai tsarki a duniya.
A cewarsa, baya ga goyon baya, ya kasance yana bibiyar ayyukan Gwamna Zulum cikin shekarun nan don haka yana farin ciki da yin tarayya da gwamnatinsa.