Shugaban Darikar Katolika a yankin Jos, Rabaran Matthew Ishaya Audu, ya raba wa Musulmi buhunan shinkafa 107 domin su yi abincin Karamar Sallah.
Rabaran Audu ya ce ya yi rabon shinkafar ce da sunan cibiyarsa ta wanzar da zaman lafiya (DREP) da nufin kyautata dangantaka tsakanin Musulmi da Kiristoci a Jihar Filato.
- Yadda aka ceto masu Sallar Tahajjud da aka yi garkuwa da su
- Amarya ta fasa aure saboda ango ya fadi jarabawar lissafi
- Abaya: Yadda gasar kayan Sallah ke sanya mata a hadari
Ya ce ya yi hakan ne ta hanyar bayar da tallafin ga bayan zakulo al’ummomi da kungiyoyin Musulmi da suka bayar da gudunmawa ga kokarinsa na kawo zaman lafiya a yankunan Jihar.
Kungiyoyin Musulumin da suka samu tallafin sun hada da Jama’atul Nasril Islam, Izala, Kungiyar Miyetti Allah, Kungiyar mata Musulmi ta FOMWAN, NASFAT, NACOMYO, Rahatul Islam, da sauransu.
A magana ta bakin Daraktan DREP, Rabaran Blaise Agwom, Audu ya ce duk da cewa abincin ba yawa, zai taimaka wasu Musulmin su samu abincin Sallah.
Limamin na Katolika ya kara da yin addu’ar neman samun zaman lafiya, inda ya bukaci matasa su nisanci ayyukan laifi musamman a lokacin bukukuwan sallah, wanda lokaci ne na komawa ga Allah.
Da yake jawabi a madadin al’ummomi da kungiyoyin Musulmi, Alhaji Sani Mudi, ya yaba masa bisa yadda yake mu’amala da kuma taya su murna a lokacin bukukuwa irin haka.
Ya ce tallafin zai taka muhimmiyar rawa wajen sanya farin ciki a zukatan mabukata a lokacin Sallah.
Mudi, wanda shi ne kakakin kungiyar JNI a Jihar Filato ya kara da cewa taimakon ya kyauta alaka tsakanin mabiya addinan biyu da wanzuwar zaman lafiya a tsakaninsu.