An shiga firgici da tashin hankali yayin da wani limamin coci a yankin Onikoko da ke Jihar Ogun ya mutu yana tsaka da wa’azi kan masu tsafi don yin arziki.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, limamin cocin Evangelical Church Winning All (ECWA) mai suna Francis Ogunnusi ya yanke jiki ya fadi yayin da yake gabatar da hudubarsa ta hani kan kokarin yin arziki cikin gaggawa kuma ko ta hali kaka.
- PDP na taro kan yankin da zai fitar da dan takarar shugaban kasa
- Har yanzu ban ayyana tsayawa wata takara ba a 2023 —Malami
Cikin wani hoton bidiyo da aka nada ya nuna yadda limamin da wani mai yi masa tafinta a gefe yake gargadi kan yawaitar kashe-kashe don tsafi a Jihar.
Bayanai sun ce mutane sun shiga cikin rudani yayin da Mista Francis ya yanke jiki ya fadi yana rike da lasifika.
An dai yi gaggawar mika shi Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Idi Aba, inda a nan mahukunta suka tabbatar da cewa ya riga mu gidan gaskiya.
Ana dai fama da matsalar kashe-kashe don yin tsafi a Jihar Ogun da wasu sassa musamman a Kudancin Najeriya.
Rahotanni sun bayyana cewa ko a watan da ya gabata an kashe wasu mutum uku don yin tsafi da zummar samun arziki a wasu yankuna daban-daban a Jihar Ogun.
A bayan nan ne Majalisar Wakilai ta nemi Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ayyana dokar ta-baci kan aikata kashe-kashe don yin tsafi a fadin kasar.
Kiran na cikin kudirorin da wakilan suka cimma a wani zama da suka yi tun a farkon watan Fabrairun da ya gabata, bayan gabatar da wani kudirin gaggawa kan rayuwar jama’a mai taken ‘Bukatar dakile kisan gilla don aikata tsafi a Najeriya’.