’Yan bindiga na ci gaba da tsare wani limami da mamunsa da suka yi awon gaba da su a masallacin Juma’a a Jihar Zamfara.
Limaman Dutsen Gari na tsaka da gabatar da hudubar Juma’a ne maharan suka yi wa masallacin kawanya suka tafi da wasu daga cikin masallatan.
- Garejin Abuja da mata zalla ke aikin gyaran mota
- Atiku ya yi takaicin sake karyewar arzikin Najeriya
- Tagwaye masu kama da juna sun angwance da mata irinsu a Kano
“Da suka kai su daji sai suka kira jerin sunayen mutun 20 da suka riga suka tsara, suka kashe biyar sannan suka saki sauran”, inji Barista Bulama Bukarti.
Bulama, mai sharhi kan tsaro da bincike kan ta’addanci, ta shafinsa na Twitter ya ce sama da mutum 100 ne aka fara daukewa a masallacin kafin a sako wasu.
Mazauna sun ce an kashe mutum biyar a lokacin harin da ’yan bindigar su fiye da 100 a kan babura suka far wa masallacin.
A ranar Lahadi ’yan sanda suka tabbatar da harin da mutwar mutum biyar din amma suka ce mutum 18 ne aka yi garkuwa da su.
Wata majiya ta ce maharan sun je ne da nufin kama wani attajiri domin karbar kudin fansa mai tsoka.
Wasu rahotanni na cewa ’yan bindigar sun sako limamin saboda ba shi da kumbar susa, amma ’yan sanda ba su tabbatar da hakan ba.
Wani mazaunin garin, Halilu Adamu, ya ce yana cikin masallacin lokacin da aka kai harin, amma ya tsallake rijiya da baya.
“Da na samu labari cewa ’yan bindiga a kan babura sun tunkaro garin, sai na yi sauri na fice daga masallaci na je gida kulle kaina”, inji shi.
Ya ce, “Ina cikin sauraron huduba sai yayana ya rada min cewa ’yan bindiga na kawo wa garin hari; daga cikin gidana na rika jin karar harbi.
“Kanena daga cikin wadanda suka sace kuma har yanzu ba mu ji daga gare su ba, ko za su nemi kudin fansa”, inji shi.
“Yawancin kauyukan masu makwabtaka da mu an kai musu hari an sace mutane da dabbobi.
“Mun shiga tashin hankali, kowa sai ta kansa yake ta yi”, inij wata majiya.
Ta ce an ga jiragen yaki na shawagi a saman kauyen amma babu tabbaci ko ya kai wa sansanin ’yan bindigar hari.
“Ya yi shawagi na dan lokaci sannan ya tafi”, inji majiyar.
Kakakin ‘Yan Sanda a Jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, ya ce mutum 18 ne maharan suka yi awon gaba da su a harin.
Ya ce tuni aka fara aiki kubutar da mutanen daga hannun ’yan bindigar.
Mazauna yankin na Karamar Hukumar Maru sun ce ’yan bindigar kan kai hari ne daga sansaninsu a cikin Daji Rugu da ke da iyaka da jihohin Katsina, Zamfara, Kaduna da kuma Neja.
A makonnin da suka gabata, ’yan bindiga sun sace mata 26 da suka hada da kananan yara da ’yan mata da matan aure daga Jihar Katsina zuwa daji a Jihar Zamfara inda suka ci zarafinu.
Daga baya sun saki matan bayan iyalansu sun sayar da kadarorinsu sun biya kudin fansa.
Baya ga girke jami’an tsaro, an jima ana tattaunawa tsakanin hukumomin jihohin Zamfara da Katsaina da ’yan bindigar amma har yanzu ba su daina kai hare-hare ba.