Allah Ya yi wa Sheikh Muhammad Khaleel Al-Qari, daya daga cikin limaman Masallacin Manzon Allah (SAW) da ke Madina, rasuwa.
Kafin wayewar garin Litinin Allah Ya yi wa malamin rasuwa, kamar yadda Hukumar Gudanarwar Masallatan Harami da na Madina ta sanar ta shafinta.
- Yakin Sudan darasi ne ga Najeriya —NSCIA
- NAJERIYA A YAU: Yadda Kamfanin Jiragen AA Rano Zai Shafi Tattalin Arzikin Najeriya
Ta bayyana cewa za a gudanar da Sallar Jana’izar malamin da Magriba, idan Allah Ya kai mu.
Sheikh Muhammad Khaleel Al-Qari yana daga cikin limamai baki da ke jagoracin Sallar Tarawih a masallacin, da ke karbar bakuncin miliyoyin masu ziyara a duk shekara.
Dan uwansa, Sheikh Mahmoud Khalil Al-Qari limami ne a Masallacin Manzon (SAW), haka kuma mahaifinsu, marigayi Sheikh Sheikh Khalil Abdul Rahman Al-Qari.
Mahaifin nasu kuma shi ne malamin fitattun makarantan Al-Qur’ani na duniya irin su, Sheikh Muhammad Ayyub da Sheikh Ali Abdullah Jaber da kuma Sheikh Abdullah Basfar.