✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yakin Sudan darasi ne ga Najeriya —NSCIA

Majalisar kolin ta kuma yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta tura rundunar samar da zaman lafiya zuwa Sudan

Majalisar Koli kan Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA) ta jaddada muhimmancin Najeriya da ta dauki darashi daga yakin da ya barke a kassar Sudan. 

Majalisar, wadda Sarkin Muslumi, Muhammad Sa’ad Abubakar yake jagoranta, ta ce abin da ke faruwa a Sudan jan hankali ne ga shugabannin Najeriya su yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a kasar.

Sanarwar da Daraktan Mulki na Majalisar, Zubairu Haruna Usman-Ugwu, ya fitar ta ce: “Mai hankali yakan dauki izina daga abin da ya faru da wani tun kafin ya same shi, ba sai abin ya same shi ba.

“Kada mu bari sai mun shiga yanayin da mutanen Sudan suke ciki sannan mu fahimcin halin da suke ciki. Mu hada hannu mu taimake su da kuma kanmu daga fadawa daga cikin irin wannan rikici.”

Ya bayyana cewa lokacin siyasa ya wuce, lokaci ne da jagoranci, saboda haka wajibi ne shugabanni da sauran masu fada-a-ji a Najeriya su dage wajen ganin tabbatuwar kasar a dunkule tare da kawo ci gaba.

Sanarwar ta bayyana cewa duk abin da zai faru, kada shugabanni da ’yan siyasa su kuskura su yi wautar sarayar da zaman lafiyar Najeriya domin biyan bukatunsu ko na mabiyansu.

Majalisar kolin ta kuma yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta tura rundunar samar da zaman lafiya zuwa Sudan domin hana rikicin yaduwar da za ta wargaza zaman lafiya a daukacin yankin Sahel.

Ta kuma yaba wa Gwamnatin Tarayya bisa kokarin da take yi na kwaso ’yan Najeriya da suka makale a Sudan kamar yadda aka yi bayan barkewar yakin Ukraine.