✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Lilin Baba zai angwance da Ummi Rahab

Ummi ta rubuta wa Lilin Baba sako cewa, “...Abin kaunata. Lallai kai ne na gaba a cikin mutane mijina a nan gaba."

Mawaki kuma jarumi Shu’aibu Ahmed Abbas, wanda aka fi sani da Lilin Baba ne ya bayyana cewa ya kusa yin wuff da jaruma Ummi Rahab.

A sakonsa na taya jarumar murnar zagoyowar ranar haihuwarta, Lilin Baba ya ce, “Ina taya murnar zagoyowar ranar haihuwarki abar kaunata, Ummi Rahab. Lallai ke mutumiyar kirki ce mai zuciyar zinare.

“Ina aika miki da sako na musamman na taya ki murnar zagayowar ranar haihuwarki a daidai lokacin da kika kara shekara daya a rayuwarki.

“Ina fata yau ya zama ranar farin ciki a gare ki da murna. Lallai a kai ban sha’awar ganin yadda kike samun cigaba a rayuwarki. Allah Ya kara wa rayuwarki albarka.”

A karshe sai ya rubuta, “Na kusa na yi wuff da ke In sha Allah.”

A kasan rubutun, jarumar ta mayar da martani, inda ta ce, “Ina godiya abin kaunata. Lallai kai ne na gaba a cikin mutane mijina a nan gaba, kuma har na kosa in ga ranar. Allah Ya nuna mana.