Mawaki kuma jarumi Shu’aibu Ahmed Abbas, wanda aka fi sani da Lilin Baba ne ya bayyana cewa ya kusa yin wuff da jaruma Ummi Rahab.
A sakonsa na taya jarumar murnar zagoyowar ranar haihuwarta, Lilin Baba ya ce, “Ina taya murnar zagoyowar ranar haihuwarki abar kaunata, Ummi Rahab. Lallai ke mutumiyar kirki ce mai zuciyar zinare.
- Zama matar Adam Zango ya jawo min koma-baya –Amina Rani
- Abin da ya hada ni da Adam A. Zango —Ummi Rahab
“Ina aika miki da sako na musamman na taya ki murnar zagayowar ranar haihuwarki a daidai lokacin da kika kara shekara daya a rayuwarki.
“Ina fata yau ya zama ranar farin ciki a gare ki da murna. Lallai a kai ban sha’awar ganin yadda kike samun cigaba a rayuwarki. Allah Ya kara wa rayuwarki albarka.”
A karshe sai ya rubuta, “Na kusa na yi wuff da ke In sha Allah.”
A kasan rubutun, jarumar ta mayar da martani, inda ta ce, “Ina godiya abin kaunata. Lallai kai ne na gaba a cikin mutane mijina a nan gaba, kuma har na kosa in ga ranar. Allah Ya nuna mana.”