Yayin da ake tsaka da yaki da cutar coronavirus a Najeriya, likitocin kasar sun ce za su tsunduma yajin aikin sai abin da hali ya yi.
Kungiyar Likitoci ta Najeriya ta ce yajin aikin nata wanda zai fara daga ranar Litinin 15 ga watan Yuni zai kunshi likitocin da ke yaki da cutar coronavirus da sauran cututtuka masu bukatar kulawar gaggawa.
Shugaban Kungiyar na kasa, Dakta Aliyu Sokomba wanda ya bayyana matsayin nasu a wata wasika, ya kuma ce annobar COVID-19 ba za ta hana su tsunduma yajin aikin ba.
- Likitoci 113 sun kamu da coronavirus a Najeriya
- Ma’aikatan lafiya na yajin aiki duk da barazanar Korona
Shugaban kungiyar wadda ke matsayin uwar kungiyoyin likitocin asibitocin gwamnati ya kuma ce “Yajin aikin namu na sai baba-ta-gani ne.
“Babu wanda zai fito aiki, kama daga masu jinyar masu cutar COVID-19 zuwa masu kula da wasu cututtuka da ke bukatar kulawar gaggawa.
“Mun umarci dukkan likitoci da sauran manyan ma’aikatan lafiya cewa su ma su bi sahu da zarar an fara yajin aikin”, in ji sanarwar.
Kungiyar ta kuma jajanta wa ‘yan Najeriya kan irin halin da za su iya fadawa da zarar ta fara yajin aikin a mako mai zuwa.
Ta kara da yin Allah-wadai da irin halin ko-in-kula da ta ce gwamnati ke nuna wa bangaren lafiya na kasar.
Ta kuma koka kan mawuyacin yanayin aiki da mambobinta ke ciki musamman wadanda ke aiki a cibiyoyin lafiya mallakar jihohi.
Ko a kwanakin baya sai da reshen Babban Birnin Tarayya na kungiyar ya shiga yajin aikin a farkon bullar annobar a Najeriya bisa dalilan kin biyan hakkoki ma’aikatan lafiya.