Kungiyar Likitoci ta NARD ta ce za ta tsunduma sabon yajin aikin gama-gari a fadin Najeriya daga a ranar Litinin, 2 ga watan Agusta, 2021.
Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar ranar Asabar bayan taron Majalisar Zatartarwa da ta gudanar a garin Umuahia, Jihar Abiya.
Kungiyar ta ce ta dauki matakin ne saboda gazawar Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi wajen biyan bukatunta da kuma rashin aiwatar da yarjejeniyar aiki da suka kulla bayan kwana 113.
Kungiyar likitocin ta janye yakin aikin gama-garin da ta tsunduma a ranar 1 zuwa 12 ga Afrilun wannan shekara, bayan kulla yarjejeniya tsakaninta da Ministan Ayyuka, Chris Ngige.
“Bayan duba na tsanaki da muka yi kan rashin martaba yarjejeniyar da muka kulla tsakaninmu da gwamnati kan abubuwan da suke damun mambobinmu bayan ajiye yajin aiki da kwana 113; Mun yanke shawarar sake tsunduma yajin aiki da misalin karfe 8 na safiyar ranar Litinin, 2 ga wagan Agusta 2021,” inji sanarwar kungiyar.
Sake shiga yajin aikin ya biyo bayan gazawar gwamnati wajen biyan wasu daga cikin likitocin albashinsu da alawus-alawus, ciki har da alawus din yaki da cutar COVID-19.