Kungiyar Ma’aikatan Lafiya ta Najeriya (NARD) ta janye yajin aikinta da ta fara a fadin kasar.
NARD bayan taron Majalisar Zartarwata ta Kasa ta sanar da cewar ma’aikatan lafiya za su koma bakin aikinsu daga karfe 8 na safiyar Juma’a 11 ga Satumba, 2020.
- Likitoci sun ceto ran kunkuru mai shekara 79 a Sakkwato
- Mai jego da jaririnta sun kubuta daga hannun ‘yan bindiga
Sanarwar da Shugaban Kungiyar, Dakata Aliyu Sokomba ya sa wa hannu, ta ce duk da haka, ma’aikatan lafiya a rassanta na jihohi da ba a samu cigaba a yanayin aikinsu ba su ci gaba da yajin aikin, su jira matakin da za a dauka cikin mako biyu.
A ranar Litininin 7 ga Satumba ne ma’aikatan lafiyan suka fara yajin aiki saboda rashin biya hakkokinsu.
Hakkokin nasu sun hada da kudin horon karo ilimi da aka ware a kasafin 2020 da kuma insohrar rayuwa ga dukkanin ma’aikatan lafiya da bashin alawus din yaki da COVID-19 da dai sauransu.
Kungiyar ta ce ta janye yajin aikin ne saboda ganin alamun da Gwamnatin Tarayya ta nuna na biyan bukatunta.
Ta ce gwamantin ta fitar da Naira biliyan 8.9 domin biyan bashin alawus din watannin Afrilu da Mayu da Yuni na yaki da COVID-19 ga dukkannin ma’aikatan lafiya.
Gwamnatin ta kuma amince ta samar da inshorar rayuwa ga dukkanin ma’aikatan lafiya sannan ta yi alkawarin biyan alawus din karo ilimi cikin mako biyu.