Shakeel Afridi, Likitan da ya toni aisirin tsohon shugaban Al Ka’ida, Marigayi Osama Bin Laden, ya nemi a sake shi.
Afridi wanda ya taimaka wa hukumar leken asirin Amurka CIA gano maboyar Osama ya yi kiran da a sake shi kamar yadda lauyansa, Qamar Nadim Afridi ya zayyana wa manema labarai na BBC.
- An harbe malami yana jagorancin sallar Tarawi
- Ramadan: Kungiya ta tallafa wa masu karamin karfi 550 da kayan abinci a Kano
An yanke wa likitan hukuncin cin sarka na shekaru 23 a gidan Dan Kande bayan nasarar kashe Osama a wani simame da Amurka ta kai 10 da suka gabata.
Lauyan ya ce yana da yakinin an yi yunkurin dakatar da soke hukuncin don kaucewa wanke likitan a cikin abin da ya bayyana a matsayin karya.
Wasu da dama na zargin cewa na hukunta likitan ne saboda abin kunyar da janyo wa kasarsa ta Pakistan.
Ana iya tuna cewa, a ranar 2 ga watan Mayun 2011, shekaru goma cif kenan da suka gabata, hukumar leken asirin Amurka ta samu nasarar kashe Osama a yankin Khyber na birnin Abbotobad da ke kasar Pakistan.
Hukumar leken asirin ta yi amfani da likitan ne wajen gudanar da wata rigakafin bogi domin gano maboyar Osama.
Har ila yau, Amurka na zargin kungiyar Al Ka’ida da kitsa hare hare a cibiyar kasuwanni ta duniya da ke birnin New York inda akalla rayukan mutum sama da dubu uku suka salwanta.
Shekaru 20 kenan da Amurkan ta ce an yi amfani da jiragen sama wajen kai hare haren da suka yi sanadiyar rubtawar gine ginen na cibiyar kasuwancin mai hawa sama da dari.