✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Likita ya yi wa yarinya ‘yar shekara 11 fyade

Wani likita ya shiga tsaka mai wuya bayan zarginsa da yi wa ‘yar aikinsa mai shekaru 11 da haihuwa fyade a jihar Binuwai. Ana zargin…

Wani likita ya shiga tsaka mai wuya bayan zarginsa da yi wa ‘yar aikinsa mai shekaru 11 da haihuwa fyade a jihar Binuwai.

Ana zargin likitan mai kimamin shekaru 40 ya yi wa yarinyar fyade da karfin tsiya ne a lokacin da matarsa da ti tafiya.

Shaidu sun ce mutumin mai suna Ebele ya yi wa yarinyar raunuka a al’auranta da wasu sassan jikinta sakamakon fadan da yarinyar ta ce ta yi da shi a lokacin.

Yarinyar da ake zargin mutumin ya lalata an kawo ta gidansa ne daga kauye domin taya iyalan likitan aikace-aikacen gida da rainon ‘ya’ya, inji makwabta.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Binuwai DSP Catherine Anene ta ce suna gudanar da bincike domin gano gaskiyan lamarin na Karamar Hukumar Otukpo.

Hakan na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da nuna damuwa game da karuwa matsalar fyade da neman a hukunta masu aikata laifin a sassan Najeriya.

Ko a ranar Alhamis Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce mutum hudu da ba a san ko su wane ne ba sun yi wa wata yarinya fyade sannan suka kuma jefar da ita a karkashin wata mota.

A ranar Larabar nan da muke ciki Manajar Cibiyar Kula da Wadanda aka Yi wa Fyade ta Jihar Adamawa, Dokta Usha Saxena, ta ce an yi fyade akalla guda 299 a cikin wata biyar a jihar Adamawa.

A baya-bayan na an yi ta samun labarin yi wa jarirai da kananan yara da ‘yan mata har ma da tsofaffi fyade.

Wasu daga cikin wadanda ake zargi da laifin iyaye ne, ko makusanta ga matan masu rauni. A wani lokaci kuma tsoffi da majiya karfi ne ake zargi da laifin.