✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Likita daya ne ke duba marasa lafiya 16,529 a Kano’

Wata kwararriyar likitar kananan yara a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano da ke Kano, Dokta Hadiza Ashiru Usman, ta ce akalla likita daya ne ke duba marasa lafiya 16,529 a…

Wata kwararriyar likitar kananan yara a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano da ke Kano, Dokta Hadiza Ashiru Usman, ta ce akalla likita daya ne ke duba marasa lafiya 16,529 a jihar.

Ta bayyana hakan ne ranar Alhamis, yayin da take gabatar da wata makala a taron masu ruwa da tsaki da Hukumar Kare Hakkin Dan Adam da Wayar da Kai (CHRICED) ta shirya a Kano.

Yayin da Kano ke da adadin mutane kusan miliyan 20, ta ce, jihar na da kwararrun likitoci 1,210 kuma ba dukansu ne ke aiki a asibitoci ba.

A cewarta, 553 daga cikin likitocin na aiki da gwamnatin Jihar, wasu a matsayin masu gudanarwa, wasu a Ma’aikatar Lafiya, wasu kuma tare da Hukumar Kula da Asibitocin da ke jihar.

Dokta Hadiza ta kuma ce, “436 suna aiki a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano, 95 a Asibitin Kashi na Dala, 41 kuma suna koyarwa da wajen duba dalibai a makarantu.

“Daga cikin wannan adadi, 105 suna aiki tare da asibitoci masu zaman kansu, wasu da kungiyoyi, wasu sun yi ritaya, wasu basa aikin kwata-kwata, yayin da kuma wasu ’yan kasuwa ne.”

Ta kara da cewar matsalar ta shafi dukkan ma’aikata da ke fannonin aikin lafiya.

Dr Hadiza Ashiru Usman ta kuma ce a fannin ma’aikatan da ke da hakkin kula da masu juna-biyu da shayarwa da ba su wuce shekaru 15 zuwa 49 ba, wanda suka kai kimanin kaso 25 cikin 100 na ilahirin al’ummar jihar, mai kula da mai shayarwa daya ce ke duba 156,250.

Tun da farko, Shugaban hukumar ta CHRICED, Ibrahim Zikrullahi, ya ce makasudin shirya taron shi ne domin tattaunawa da kuma duba matsalolin da ake fuskanta a wadannan fannoni don a magance su.