Yayin da ake shirin gudanar da zaben shugaban kasa a Libya a ranar 24 ga watan Disamba, 2021;
Ga jerin rigingimun da suka dabaibaye kasar tun bayan hambarar da Shugaba Muammar Gaddafi a shekarar 2011.
- Sarauniyar Kyau: Har yanzu ji nake kamar a mafarki —Shatu Garko
- Gobara ta kone kamfanin sayar da kayan gado a Kano
– 2011: Mutuwar Gaddafi –
- Guguwar sauyin kasashen Larabawa a Tunisiya da Masar ta ba wa ’yan Libya kwarin gwiwar gudanar da zanga-zangar neman sauyi a watan Fabrairun 2011.
- Taimakon sojin da Amurka da Faransa da Birtaniya suka ba wa masu zanga-zangar ya sa ta rikide zuwa tawaye da daukar makamai.
- Shugaba Gaddafi, wanda ya shekara 42 a kan mulki ya tsere daga Tripoli, babban birnin kasar, amma ’yan tawaye sun kama shi suka kashe shi a ranar 20 ga watan Oktoba.
- A watan Agustan 2012 ’yan tawaye sun mika mulki ga gwamnati wucin gadi (GNC).
– 2012: Hari kan ofisoshin jakadancin kasashen waje –
- An kashe Jakadan Amurka a Libya, Chris Stevens da wasu jami’an Amurka uku a harin da aka kai a Karamin Ofishin Jakadancin Amurka da ke birnin Benghazi ranar 11 ga Satumba, 2012.
- Ana zargin mayakan jihadi masu alaka da Al-Qaeda da kai harin.
- A Afrilun 2013 an kai harin bam a cikin mota Ofishin jakadancin Faransa a Tripoli, aka jikkata Faransawa biyu masu gadi.
- Yawancin jami’an diflomasiyyar kasashen waje sun bar kasar.
– 2014-2016: Gwamnatin adawa –
- An yi zaben ’yan majalisa a watan Yuni , inda aka samar da majalisar wakilai wadda masu kyamar Musulunci ke da rinjaye.
- ’Yan-sakai masu kishin Islama sun yi watsi da sakamakon zaben tare da mamaye Tripoli a watan Agusta, aka sake maido da GNC kan karagar mulki.
- Majalisar wakilan da kasashen duniya suke goyon baya ta koma da zama a birnin Tobruk a Gabashin kasar.
- An kafa Malasar Dattawa mai hamayya da Majalisar Wakilan a birnin Tripoli da ke Yammacin kasar.
- Don haka Libya ta samu kanta da gwamnatoci biyu da majalisun dokoki biyu.
- Bayan watanni ana tattaunawa, a watan Disambar 2015, majalisun da ke hamayya da juna suka kulla yarjejeniyar kafa gwamnatin sulhu a kasar Maroko.
- A watan Maris, 2016, shugaban gwamnatin, Fayez al-Sarraj, ya isa Tripoli domin kafa sabuwar gwamnati, amma madugun yakin Gabashn kasar, Khalifa Haftar, ya ki amincewa da gwamnatin.
– 2019: Hare-haren Khalifa Haftar –
- Haftar ya sanar da “cikakken ’yancin” yankin Benghazi daga mayakan jihadi a watan Yulin 2017, bayan sama da shekara uku ana gwabza fada.
- A watan Janairun 2019 ya fara kai hari a Kudancin Libya mai arzikin mai, ya kwace Sebha, babban birnin yankin da wani babban rijiyoyin mai na kasar.
- A watan Afrilu ya umarci mayakansa da su nausa zuwa Tripoli.
- A watan Yunin 2020, dakarun da ke Tripoli da Turkiyya ke mara wa baya suka kwace yanki karshe a Yammacin kasar da Khalifa Haftar ke iko da shi, suka fatattaki mayakan Haftar da ke samun goyon bayan Rasha, Masar da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).
– 2020-2021: Tattaunawa da fargaba –
- Hukumomi masu hamayya da juna sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta ta dindindin a watan Oktoba bayan tattaunawar da Majalisar Dinkin Duniya ta shirya a Geneva.
- Bayan wata daya kuma suka zauna a birnin Tunis, tare da amincewa a gudanar da zaben ’yan majalisar dokoki da na shugaban kasa a watan Disamban 2021.
- A watan Maris, 2021, wakilan Libya kan tafiyar da Majalisar Dinkin Duniya ta jagoranta sun amince da kafa gwamnatin hadin gwiwa karkashin Fira Ministan rikon kwarya, Abdulhamid Dbeibah, har zuwa zabe.
– Rikicin zabe –
- A watan Satumba, majalisar dokokin da ke Gabashin kasar ta amince da dokar zaben ’yan majalisar dokoki, tare da daftarin dokar zaben shugaban kasa, wanda ’yan adawa ke ganin ta ba wa Haftar fifiko.
- A Oktoba, majalisar dokoki da ke Tobruk ta amince da dokar zaben tare da tsayar 24 ga Disamba a matsayin ranar da zaben shugaban kasa; Amma ta dage zaben ’yan majalisa zuwa watan Janairun 2022.
- Taron manyan kasashen duniya a birnin Paris na kasar Faransa a tsakiyar watan Nuwamba ya bukaci shugabannin Libya da su bi jadawalin zaben, tare da umartar sojojin haya na kasashen waje su fice daga Libya.
- Dan Gaddafi, Seif al-Islam, ya fito takara kamar Dbeibah, kuma Haftar ya tabbatar da cewa shi ma zai tsaya takarar.
- Hakan ya kawo rarrabuwar kai kan wanda ya kamata ya tsaya takara.
- A karshen watan Nuwamba, Ministan Harkokin Cikin Gidan Libya, Khaled Mazen, ya ce akwai yiwuwar dage zaben shugaban kasan, muddin aka ci gaba da karya doka da ke barazana ga tsarin zaben, a yayin da Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya ce ba ya son zaben ya samu alaka da matsalar.
- Duk da cewa hukumar zaben kasar Libya ta jinkirta bayyana jerin sunayen ’yan takara na karshe a ranar Asabar, a ranar Lahadi, shugaban rikon kwaryar kasar, Ramadan Abu Jnah, ya dage cewa za a gudanar da zaben kuma “kada wai ya hana ’yan Libya gudanar da zabe mai cike da tarihi.”