Ƙungiyar WISE da ake zargi da ayyukan ‘yan maɗigo da ‘yan luwaɗi a Jihar Kano, ta jima tana gudanar da ayyukanta da sunan tallafa wa mata.
Majiyarmu wadda ta buƙaci a sakaya sunanta, ta tabbatar da cewar ƙungiyar ta taɓa kai wa Hisbah ziyara da sunan ƙulla alaƙar aiki domin tallafa wa mata da masu ƙaramin ƙarfi.
- An ɗaure malami shekara 20 kan sukar gwamnati a Saudiyya
- Tinubu ya ƙirƙiro ma’aikatar harkokin kiwon dabbobi
Majiyar ta ce ƙungiyar ta raba kayan abinci a watan azumin Ramadan da ya gabata.
“Wannan ƙungiyar ta ziyarci ofishin Hisbah a lokacin Ramadan har ta raba kayan abinci ga mata da mabuƙata.
“Wannan ba ita kaɗai ba ce ƙungiyar da Hisbah ke nema don tantance ayyukansu ba,” in ji majiyar.
An ruwaito cewar ƙungiyar WISE ta bar Kano bayan da gwamnatin jihar ta bai wa Hisbah umarnin bankaɗo ayyukanta.
Aminiya ta yi ƙoƙarin gano ofishin ƙungiyar wanda aka bayyana a lamba 239 Jigirya a unguwar ’Yankaba a kan titin Hadeja, amma babu wannan adireshi.
Wasu daga cikin mazauna unguwar sun bayyana cewar ba su san da ƙungiyar ba.
Aminiya ta ruwaito yadda gwamnatin jihar ta bayar da umarnin fatattar ƙungiyoyin da ke koyar da maɗigo da luwaɗi, bayan ganin wani jami’in hukumar Hisbah a cikin wani bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta.