Kungiyar Kwallon Kafa ta Leeds United ta raba gari da kocinta, Marcelo Bielsa sakamakon yadda abubuwa suka tabarbare a bayan nan.
Wannan na zuwa ne a sakamakon kashin da Leeds ta sha na ci 4-0 a hannun Tottenham, wanda shi ne cikon shan kashi wasa hudu a jere.
A wata sanarwar da Shugaban Leeds Andrea Radrizzani ya fitar a ranar Lahadi, ya ce sun yanke shawarar yanke kauna da kocin ne saboda yadda abubuwa suka tabarbare.
“Mun samu kanmu a matsayi marar kyau, kuma ina ganin yanzu lokaci ne da ya kamata mu karo sabon koci domin ya yi tasiri a wannan lokaci na wannan kaka mafi kalubale,” in ji Radrizzani
Marcelo Bielsa dan kasar Argentina mai shekara 66 ya karbi aikin horar da Leeds ne a watan Yunin 2018, kuma yanzu ya tafi yar bar kungiyar da tazarar maki biyu tsakaninta da kasan teburin gasar Firimiyar Ingila ta bana.
A bara, karƙashin jagorancin Bielsa, Leeds ta kammala kaka a matsayi na tara, shekarar da ta hauro gasar Firimiyar bayan shafe shekara 16 ba ta gasar.