Shugaban Majalisar Dattijai, Ahmad Lawan ya kalubalanci yadda Gwamnatin Tarayya ta rattaba hannu a kan dokar cefanar da bangaren wutar lantarki a shekara ta 2013.
A shekarar ta 2013 ce dai aka kacaccala Kamfanin da ke Kula harkar Lantarki na Kasa (PHCN) wanda ya share fagen samuwar kamfanonin samar da hasken lantarki guda shida, kamfanonin rarraba ta guda 11 da kuma kamfanin da ke kula da dakonta (TCN).
Dukkan kamfanonin da ke kula da samarwa tare da rarraba wutar dai a yanzu haka mallakin ‘yan kasuwa ne.
Lawan ya yi takaicin cewa ‘yan Najeriya da dama sun tsammaci ganin ingantuwar wutar bayan cefanar da bangaren, amma har yanzu ba ta sauya zane ba.
Shugaban majalisar y a yi wadannan kalaman ne yayin da yake bude zaman jin ra’ayoyin jama’a da Kwamitin Lantarki na Majalisar ya shirya don tattauna yadda za a inganta ta da kuma duba kan irin barnar da annobar coronavirus ta yi wa bangaren.
Lawan ya kara da cewa, “Ta yaya ma suka sa hannu a yarjejeniyar ta makudan kudade ba tare da an nuna musu bakin bindiga ba, duk da cewa mun san ba za mu iya samar da wutar ba?
“Kamata ya yi tun farko kada mu rattaba hannu tunda mun san ba za mu iya ba. Yanzu ga shi an sa dole mu yi aman Naira biliyan 14 duk wata. A kan wanne dalili?
“Sai da Bankin Duniya ya ja kunnenmu a kai amma muka yi kememe. Yanzu da wace fuska za mu je mu ce ya tallafa mana? Wannan shi ne abin da nake hange.
“Dole a yi wani abu a kai, saboda a matsayinmu na shugabanni mu ke da alhakin duk abin da ya faru” inji shugaban majalisar.
Ya kuma umarci kwamitin na lantarki da ya yi zuzzurfan bincike kan abubuwan da suka wakana a yayin cinikayyar.