✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Lauya na neman gwamnati ta biya shi diyyar N10m saboda kafa shinge a hanya

Hakan, cewar lauyan tarnaki ne ga ’yancinsa na watayawa.

Wani lauya mai fafutukar kare hakkin dan Adam, Francis Moneke ya maka Gwamnatin Jihar Anambra a gaban kotu yana neman a biya shi diyyar Naira miliyan 10 saboda kafa shinge a kan hanya.

 A cewar lauyan, hakan yin tarnaki ne ga ’yancinsa na watayawa da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya ba shi.

Yana dai karar Gwamnatin Jihar ne da Babban Lauyan Gwamnati kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar da kuma Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar saboda rufe hanyar Ziki Avenue da ke Awka, babban birnin Jihar.

Ya ce an kafa shingayen ne a tsakanin gidan mai na Ifenna da kuma shatale-talen Amawbia da ke kan titin na Zik Avenue da kuma kan hanyar Amwbia zuwa Nibo zuwa kofar shiga masaukin Gwamnan Jihar da ke Amambia.

Lauyan dai ya yi ikirarin cewa shingayen wadanda aka kafa tsawon watanni sun jawo masa wahala matuka a ranakun 14 da 20 ga watan Agustan 2021.

A cewarsa, “Sashe na 41(1) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 ya ba kowanne dan Najeriya ’yancin watayawa ba tare da kowanne irin tarnaki ba ko na zama a duk inda yake so ba tare da an takura masa ba.”

A cikin karar da ya shigar a Babbar Kotun da ke Awka mai lamba A/MISC194/2021, lauyan ya kalubalanci tare hanyar wanda ya ce an yi ne da umarnin Gwamna da kuma Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar.

Ya roki kotun da ta tilasta wa wadanda yake karar su cire shingayen tare da bude dukkan hanyoyin domin ba jama’ar Jihar damar zirga-zirgarsu yadda ya kamata.

Francis ya kuma roketa da ta sa wadanda yake karar da su yi karo ko kuma a dunkule su biya shi Naira miliyan 10 saboda abin da ya kira tauye masa hakkinsa na watayawa kamar yadda Kundin Tsarin Mulki ya bashi.