✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Lata Mangeshkar: Fitacciyar mawakiyar India ta rasu

Gwamnatin India ta ayyana hutun kwanaki biyu na makokin Lata Mangeshkar.

Rahotanni daga kasar India sun bayyana cewa Allah Ya yi wa fitacciyar mawakiya kuma daya daga cikin mawakan da ake girmamawa a kasar, Lata Mangeshkar rasuwa.

Mawakiyar ta rasu ne tana da shekaru 92 da haihuwa inda likitoci a wani asibiti a Mumbai suka tabbatar da cewa cutar Coronavirus ce ta yi ajalinta.

Likitocin da suka yi mata magani a lokacin tana asibitin sun ce ta samu matsala ne da wasu daga cikin sassan jikinta kamar huhu.

Tuni dai gwamnatin India ta ayyana hutun kwanaki biyu na makokin wannan fitacciyar mawakiya gami da sauke tutar kasar domin karrama ta.

Mawakiya Lata Mangeshkar ita ce mawakiyar da ta ke waka a cikin harsuna 36 na kasar India da ma na wasu kasashen waje.

Tarihin Lata Mangeshkar a takaice

An haifi mawakiyar ne a ranar 28 ga watan Satumbar 1929 a jihar Madhya Pradesh.

Sunanta na ainihi Hema Hardikar Mangeshkar, kuma ita ce babba a wajen iyayenta inda ta ke da kanne uku.

Tun tana shekara biyar da haihuwa ta fara fitowa a wasu wakoki na mahaifinta, koda ya ke ba wakar ta ke ba a lokacin.

Tun tana karama ta ke da sha’awar waka, hakan ya ba wa mahaifinta damar karfafa mata gwiwa a kan abinda ta ke so.

Mahaifinta ya rasu a lokacin tana ’yar shekara 13 a duniya, inda wani amininsa ya ci gaba da dawainiya da ita da sauran ’yan uwanta, har ma ya taimaka mata wajen cimma burinta na zama mawakiya.

Wakarta ta farko da ta tayi fice a fina-finan Hindu, itace wadda ta yi a shekarar 1948 a fim din Majboor wato wakar “Dil Mera Toda, Mujhe Kahin Ka Na Chhora”.

Lata Mangeshkar ta samu lambobin yabo da dama ciki har da National Film Awards uku da Filmfare awards shida da dai sauransu.

%d bloggers like this: