Hukumar Kula da Zirga-Zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA), ta ce daga yanzu duk masu bukatar lasisin tuka babur din ‘A Daidaita Sahu’ a Jihar dole ne su biya Naira dubu dari madadin Naira dubu takwas da ake biya a baya.
Shugaban Hukumar, Baffa Babba Dan Agundi ne ya sanar da hakan a yayin ganawarsa da manema labarai ranar Laraba a birnin Dabo.
Ya ce, “Duk wadanda ba su yi rajistar neman izinin tuka babur mai kafa uku tun a baya ba, to kuwa a yanzu duk mai so ya koma Naira dubu dari,” a cewarsa.
Ya ce sun baza jami’ansu domin lura da kuma cafke wadanda ba su da lasisin da zummar daukar mataki a kansu.
A cewarsa, Gwamnatin Jihar ta bayar da isasshen lokaci amma wasu masu kunnen kashi suka suka ki yi a kan lokacin da aka bayar.
Dan Agundi ya ce a yanzu akwai baburan ‘A Daidaita Sahu’ dubu sittin masu lasisi da ake harkokin sufuri da su a Jihar Kano.
Dangane da batun karbar haraji, Dan Agundi ya ce Hukumar Tattara Haraji ta Jihar Kano ce ke da alhakin karba a yayin da nauyin da rataya a kan tasu hukumar ya takaita kadai a kan aiwatarwa.